1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shekaru 30 da kisan Saro-Wiwa

Muhammad Bello SB
November 10, 2025

A Ogoni da ke yankin Niger Delta na Najeriya ana tunawa da ranar 10 ga watan Nuwamba kowace shekara, ranar ke nan da aka kashe dan fafutukar kare muhalli kuma marubuci, Ken Saro-Wiwa inda aka cika shekaru 30 ke nan.

Najeriya 1993 | Ken Saro-Wiwa
Ken Saro-WiwaHoto: AFP/Greenpeace/dpa/picture alliance

Ana tunawa da ranar ta 10 ga watan Nuwamba na kowace shekara da al'ummar Ogoni a yankin Niger Delta kan yi, kisan sanannen marubucin kuma dan gwagwarmayar yankin,Ken Saro-Wiwa, wanda gwamnatin Najeriya ta sahale rataye shi har lahira, tare da wasu mukarrabansa takwas.

Dalilin hukuncin

Marigayi Janar Sani Abacha tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojan NajeriyaHoto: AFP/dpa/picture alliance

Haka ya biyo bayan wani hukuncin zaman shari'a da ya yanke musu hukuncin kisa shekaru 30 da suka wuce, karkashin jagorancin mulkin soja a lokacin. Kungiyoyin kare muhalli, da kare hakkin dan Adam, gami da mutanen yankin Ogoni, na kan gaba wajen gudanar da wannan tunawa. Lamarin ya faru lokacin da shugaban gwamnatin mulkin soja Janar Sani Abacha yake rike da madafun ikon kasar.

Ken Saro-Wiwa da aka rataye har lahira, sakamakon hukunci kan laifi da aka tabbatar kansa, bayan tabbatar da laifin nasa tare da wasu mukarrabansa takwas a yankin, bayan wata mummunar zanga-zanga da suka yi jallin haifarwa a yankin na Ogoni, ta janyo kisan wasu manyan sarakuna hudu na Ogoni, hukuncin kuma da a'lummar Ogoni ba ta aminta da ita ba har yanzu.

Makasudin rikicin

Zanga-zangar adawa da kisan Ken Saro-Wiwa da aka yi a Jamus lokacinHoto: Oliver Multhaup/dpa/picture alliance

Rikice-rikice dai a yankin na Ogoni, yayin da Ken Saro-Wiwa na da rai, sun kasance rikice-rikice ne tsakanin al'ummar Ogoni da kuma Kamfanonin mai da ke aiki a yankin da kuma al'ummar ke zargin kamfanonin da barnata musu muhalli, durkusar da ayyukan gona da gurbata ruwan koguna da teku da suke sana'arsu ta kamun kifi, tare ma da ikirarin ba sa amfana daga dimbin arzikin na mai da Kamfanonin na mai ke hakowa a yankin.

A ranar 10 ga watan Nuwamba na 1995, an rataye Ken Saro-Wiwa tare da mutane takwas, kisan kuma da ya jawo cece-kuce a ciki da ma kasashen duniya.