1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben gwamna a jihar Edon Najeriya

September 16, 2020

Daga dukkan alamu tsare-tsare sun kankama dangane da zaben kujerar gwamna a jihar Edo da ke Najeriya, zaben da ake sa ran zai gudana a karshen mako.

Nigeria wählt Gouverneure und Regionalparlamente
shirye-shiryen gudanar da zabe a jihar Edo da ke NajeriyaHoto: Reuters/Penney

Ana dai kokarin dinke dukkanin bararakar da ke akwai, da ka iya haifar da tashe-tashen hankula a yayin zaben na gwamna, da ake shirin gudanarwa a ranar 19 ga wannan wata na Satumba da muke ciki. Tuni dai hankulan al'umma a ciki da wajen Najeriyar, ya karkata kan yadda wannan zabe zai gudana, musamman ma ganin yadda 'yan siyasar Najeriyar ke kallon zaben a matsayin zakaran gwajin dafi, dangane da al'kiblar siyasar kasar da ma inda hankulan 'yan Najeriyar ka iya karkata a siyasar 2023.

A baya-bayan nan dai rikici ya barke a jihar ta Edo, rikicin kuma da ake wa kallon ba ya rasa nasaba da tunanin inda rana za ta fadi a kakar siyasar ta 2023, inda ake ganin shi ne dalilin 'yan siyasar na tayar da hankula da har ya kai ga jikkata da ma salwantar rayuka, musamman ma a tsakankanin 'yan jamiyyun APC da PDP, da adawarsu ta fi zafafa.

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta a Najeriya, INEC ta yi gargadi kan zaben EdoHoto: DW

Dakta Nick Dazan shi ne mai magana da yawun Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa a Najeriyar wato INEC, wanda kuma ya dada jan kunne ga 'yan siyasar ta Edo, dangane da batun tashin hankali a yayin zaben. Kawo yanzu dai, 'yan takarar ta gwamna daga jam'iyyu dabam-dabam a jihar, sun sa hannun domin tabbatar da cewar za su kiyaye dokokin zabe da nufin kaucewa tayar da husuma.

Karin Bayani: PDP ta soki lamirin dage zaben Edo

Babban sifeto janar na 'yan sandan Najeriyar Mohammed Abubakar Adamu ya yi karin haske kan dokokin da aka gindaya: "Ba saka kaya mai alamar siyasa ranar zabe, babu wanda aka yadda ya yi yawo da tawagar jami'an tsaro. Idan mutum ya kada kuri'arsa, to ya koma gida ko ya tsaya nesa da inda ake zaben. Babu kai-kawo daga wannan rumfar zabe zuwa waccan,sai dai ga jami'an da doka ta yardar musu, musamman jami'an zabe da 'yan jarida. Sannan ba sayar da kayan maye a harabar inda ake zabe."
Sifeto janar na 'yan sandan dai, ya ce jami'ansa dubu 31 ne za su yi aikin tsaro yayin wannan zabe, baya ga jami'an tsaron farar hula wato Civil Defence da na 'yan sandan ciki na DSS da sojoji da za su tallafa musu. Koda yake ranar zaben ta gabato,amma hakan bai hana gwamatin tarayya karkashin jam'iyyar APC, kaddamar da wani shirin tallafawa kasuwancin mata kimanin 2000 a jihar ta Edoba, inda aka ringa rarraba musu kudi.

An tanadi jami'an tsaro domin tabbatar da doka da oda, yayin zaben jihar EdoHoto: imago/Xinhua

Karin Bayani: An koka kan amfani da kudi a zaben Ekiti

Tun a baya dai gwamnan jihar Godwin Obaseki da shi ma ke cikin jerin 'yan takara, ya koka cewar yana hangen jamiyyar APC za tai amfani da karfin gwamnatin tarayyar ,a harkokin zaben jihar. Sassan duniya dai na ci gaba da kallon yadda zaben na Edo zai kaya, inda ma har sai da masarautar Birtaniya ta yi barazanar hana duk wani dan siyasar da ya hana ruwa gudu a wannan zabe shiga kasar ta Birtaniya.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani