Najeriya: Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin 2020
October 8, 2019A badin dai gwamnatin kasar ta ce za ta kashe Naira Triliyan 10 da miliyan dubu 330 domin manyan ayyuka da tafi da harkokin yau da gobe. Hankalin gwamnatin dai a cewar shugaban kasar zai karkata ne ga kammala ayyukan da gwamnatin ta fara a sassa daban daban maimakon sabbi
“Hankalinmu zai karkata ne ga karasa ayyukan dake kasa maimakon sabbi. Ba'a yarda wata hukuma ko ma'aikata ta gwamnatin ta karbi wasu sabbin ayyuka cikin kasafin ba, har sai idan akwai cikakken tanadi na ayyukan a cikin kasafin Haka kuma mun tura duk manyan ayyukan da ba za'a iya kammalasu ba a shekarar bana zuwa kasafin badi“.
A badin dai gwamnati na sa ran samun kudin shigar da ya kai Naira Triliyan 8 da miliyan 155 a matsayin kudin shiga da mafi yawansu za su fito daga wani kari na harajin mai saye da gwamnatin ta sanar ta ke kuma shirin aiwatarwa daga shekarar da ke tafe.
Gwamnatin dai ta tsara kashe Triliyan 3.6 domin albashin ma'aikata a cikin sabon tsarin mafi karancin albashi.
Kasafin dake zaman irin sa na farko a lokaci mai nisa da ke da burin cika ka'idar kasafin kudin Janairu zuwa Disamba na nufin abubuwa daban daban a idanun ‘yan majalisun kasar daban daban.
Tarrayar Najeriyar dai na fatan kasafin zai taimaka wajen kara dadaito ga tattalin arzikin kasar wadda sannu a hankali ke kulle iyaka a matsayin sabuwar dabarar kai karshen tafiyar hawainiya ta tattalin arzikin.