Siyasa gabanin zaben 2023 a Najeriya
July 14, 2022Kamar dai yadda Malam Bahaushe ke cewa idan aski ya zo gaban goshin ya fi zafi, a yanzu ana iya cewa yayin da zabukan 2023 ke kara karatowa a Najeriya al'amuran siyasa na daukar dumi. Babban abin da ya dauki hankula a yanzu dai shi ne batun zabar mataimaki da dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar APC mai mullki Bola Ahmed Tinubu ya yi, inda ya ayyana Kashim Shettima tsohon gwamnan jihar Borno a matsayin wanda ya ke son ya marawa takarra tasa baya a matsayin mataimaki.
Najeriya: Makomar takarar Tinubu da Shettima
Wannan batu dai ya haifar da cece-kuce, ganin cewa shi dan takarar Musulmi ne kuma ya zabi Musulmi a matsayin mataimaki. A bisa al'aada dai a Najeriya, ya kan kasance idan dan takara Musulmi ne to mataimakinsa kan zama mabiyin addinin Kirista. Haka kuma idan dan takarar ya kasance Kirista to mataimakinsa kan zamo Musulmi. Hakan ce ta sanya da dama ke ganin hanyar da Tinubu ya dauko ta zabar Shettima a matsayin mataimakinsa, ba za ta zamo mai bullewa ba.
Najeriya: Buhari na son sauka daga mulki
A hannu guda kuma shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari ya yin wata hira da manema labarai, ya nunar da cewea shi fa ya kagara ya kammala mulkin Najeriyar ya mika shi ga wata gwamnati. Wannan ne dai karo na farko da aka jiyo Buharin na furta wannan kalamai, a tsawon shekaru kusan takwas da ya kwashe yana mulkar kasar. Tun bayan hawan Shugaba Buhari dai, kasar ke fama da tarin matsaloli musamman wadanda suka danganci na tsaro da matsalar tattalin arziki.