Najeriya: Barikin Marte ya koma hannun soja
January 17, 2021Talla
A cikin sanarwa da rundunar sojan Najeriya ta fitar, rundunar ta ce dakarunta na Opretion TURA TA KAI BANGO, sun fatattaki 'yan ta'addan tare da karbe iko da barikin garin mai iyaka da yankin Tafkin Chadi.
Sojan sun kuma tarwatsa motocin yakin mayakan kungiyar da dama, baya kashe da dama a yayin gumurzun da suka jima suna yi.
A yammacin Juma'ar da tagabata ce mayakan kungiyar Boko Haram reshen ISWAP suka kai farmaki a barikin soja da ke garin na Marte tare da karbe iko da barikin, lamarin da ya tilasta wa fararen hula da dama gudu don tisra da ransu a Maiduguri mai nisan kilo 130 daga yankin.