Najeriya: Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai
August 14, 2024Sojojin Najeriya sun ce sun lalata haramtattun matatun mai akalla guda 27 sannan sun kwace kimanin lita 100,000 na danyen mai da aka sato. Wannan na daga cikin jerin samame da rundunar sojin ta kaddamar a wannan makon kan barayin mai a yankin Niger Delta.
A cikin wata sanarwa sojojin sun ce jami'ansu sun lalata haramtattun matatun mai 23 a kan hanyar kogin Imo a kudu maso gabashin Najeriya wanda ta baiyana a matsayin tungar ayyukan 'yan bata gari.
Haka kuma rundunar sojin ta ce ta lalata wasu haramtattun matatun a yankin Degema kusa da birnin Port Harcourt
Kakakin rundunar sojin Laftanar Kanal Danjuma Jonah ya ce baya ga haramtattun matatun sun kuma kwace motoci da tankokin mai
Najeriya dai ita ce kan gaba a tsakanin kasashen Afirka masu arzikin mai sai dai yawan satar man da fasa bututu da ke yin zagon kasa sun sa yawan man da kasar ke hakowa ya ragu a yan shekarun baya bayan nan wanda ya sa abin da ta ke fitarwa zuwa kasuwannin duniya ya ragu ya kuma kawo nakasun kudin shiga ga gwamnatin da ma tarin kalubale ga shugaban kasar Bola Tinubu.