SiyasaAfirka
Najeriya na binciken dan sandanta Abba Kyari
July 30, 2021Talla
A cikin wata sanarwa da Frank Mba mai magana da yawun 'yan sandan Najeriya ya fitar ya ce rundunarsu ta dukufa wurin tabbatar da adalci, a don haka ta kaddamar da binciken.
A Najeriya dai ana yi wa Abba Kyari kallon mutunci a matsayin kwararren dan sanda da ya kasance dodon 'yan bindiga masu garkuwa da mutane. Kazalika masu aikata manyan laifuka a cikin birane ma na tsoron haduwa da Abba Kyarin ganin yadda ya jima yana samun galaba kan masu aikata laifuka musamman garkuwa da mutane. Tuni dai dan sandan ya musanta zargin da ake ma sa.