Najeriya ta bude filin jiragen saman Abuja
April 18, 2017Talla
An dai bude filin jirgin ne kwana guda kafin cikar wa'adin da aka deba dan kammala gyaran, inda jirgin saman kasar Habasha na Ethiopian Airlines ya zama na farko da ya fara sauka a yau Talata a filin jirin na Namdi Azikwe International Airport da ke Abuja.
Sai dai rufe filin jirgin na wuchin gadi ya janyo cece-kuce a fadin kasar ganin filin jirgin na cikin filayen jiragen sama mafi zirga-ziga a yammacin Afirka wanda masana ke ganin rashin sa ido a kan gyara ne ya haddasa matsalar wanda dakatar da shi na lokaci kadan na haifar da koma baya a harkokin tattalin arzikin Najeriya.