WasanniAfirka
Najeriya ta kai matakin kusa da na karshe
January 10, 2026
Talla
Najeriya ta samu kai wa zuwa wasan kusa da na karshe a gasar neman cin kofin Afirka bayan da ta doke kasar Aljeriya da ci 2 da nema.
Sannan tun farko a wasan da aka gudanar ranar Jumma'a, kasar Senegal ta doke Mali da ci daya mai ban haushi, yayin da Maroko mai masaukin baki ta fitar da Kamaru da ci biyu da nema. Kuma yanzu Najeriya za ta kara da Maroko mai mauakin baki a wasan kusa da na karshe. Yayin da Senagal za ta kara Masar ko Cote d'Ivoire.