1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta fusata da kyamar baki a Afirka ta Kudu

May 3, 2026

Najeriya ta gayyaci babban jami’in diflomasiyyar Afirka ta Kudu kan hare-haren da ake kai wa baki a kasar. Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun rikice-rikicen nuna kiyayya ga baƙi a Afirka ta Kudu.

Najeriya, Abuja | Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
Najeriya, Abuja | Shugaban kasa Bola Ahmed TinubuHoto: Nigerian Presidency/Handout/Anadolu/picture alliance

Gwamnatin Najeriya ta gayyaci babban jami'in diflomasiyyar Afirka ta Kudu a Abuja, sakamakon hare-haren da ake kai wa 'yan kasashen waje a kasar.

Afirka ta Kudu dai ta dade tana zama mafaka ga ma'aikatan Afirka, amma tana fama da rashin aikin yi da ya haura kashi 30 cikin 100.

An sha samun zanga-zangar nuna kiyayya ga mutanen ketare a Afirka ta Kudun, ciki har da sabbin rikice-rikicen da suka barke a makonnin baya.

Matakin Najeriya ya biyo irin wanda Ghana ta dauka, inda ta gayyaci wakilin Afirka ta Kudu a Accra kan zargin hare-hare ga 'yan kasarta.

Afirka ta Kudu dai ita ce kasar da ta fi bunkasar masana’antu a nahiyar Afirka, kuma sama da mutane miliyan uku ’yan kasashen waje ke zaune a cikinta, kusan kashi 5.1 cikin 100 na yawan jama'arta.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW