1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta kama 'yan Poland da zargi a kan ɗaga tutar Rasha

August 8, 2024

Gwamnatin Najeriya, ta kama wasu 'yan kasar Poland mutum bakwai saboda zargin su da ta yi da ɗaga tutar kasar Rasha a wannan makon a birnin Kano da ke arewacin kasar.

'Yansandan Najeriya a wajen zanga-zanga
'Yansandan Najeriya a wajen zanga-zangaHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Wannan dai labari ne da hukumar bincike ta farin kaya a Najeriyar ta tabbatar, hukumar da ta kama har da wasu telolin da suka dinka tutar ta Rasha da gomman mutane suka yi ta ɗagawa a jihar Kano da ke arewacin kasar.

Shi ma babban jami'in jakadancin kasar Poland a Najeriya, Stanislaw Gulinski ya ba da labarin kame 'yan kasar tasa a lokacin wata ganawa da ministan  harkokin wajen Najeriya a Abuja.

Dubban daruruwan 'yan Najeriya ne ke zanga-zanga tun a ranar daya ga wannan watan, saboda rashin jin dadi da yadda gwamnatin Shugaba Tinubu ke tafiyar da harkokin tattalin arziki.

Rayuwa dai ta yi wa miliyoyin 'yan Najeriyar tsauri musamman bayan janye tallafi a kan man fetir da na wutar lantarki da shugaban kasar ya yi.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty Int'l ta ce mutane 22 suka mutu a zanga-zangar a yankin arewacin Najeriya.