Najeriya ta karɓo bashi daga China
September 13, 2012![©Jonathan Rebboah/Wostok Press/Maxppp France, Paris 25/11/2011 Le president du Nigeria Goodluck Jonathan arrive au palais de l Elysee The President of Nigeria Goodluck Jonathan at the Elysee Palace](https://static.dw.com/image/15685889_800.webp)
Talla
Ƙasar China ta baiwa Tarayyar Najeriya bashin na euro miliyan 700 domin gudanar da wasu ayyuka. Daga cikin ayyukan da Najeriya za ta yi da wannan bashin sun haɗa da shinfiɗa layin dogo a babban birnin ƙasar Abuja da kuma gyara wasu filayin jiragen sama a wasu manyan biranen huɗu na ƙasar. Wani ɓangaren bashin za'a yi amfani da shi ne wajen inganta sadarwar Internet. Ƙasar China dai tana amfani da irin bada wannan basuka domin samun albarkatun ƙarƙashin ƙasar kamar su manfetur da sauransu.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Abdullahi Tanko Bala