1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasan La liga ya yi zafi

Mouhamadou Awal Balarabe SB
March 17, 2025

A Najeriya kuwa, rashin damawa da tsohon kyaftain na Super Eagles Ahmed Musa a wasannin share fagen shiga kofin duniya na kwallon kafa na ci wa wasu magoya baya tuwo a kwarya.

'Yan wasan Barcelona
Äan wasan BarcelonaHoto: Alberto Gardin/NurPhoto/picture alliance

Kungiyar kwallon kafar Barcelona ta nuna wa Atletico Madrid cewar ruwa ba sa'an kwando ba ne, inda ta mamaye ta da 4-2 a mako na 28 na gasar La Liga ta Spain. Amma dai, sai da kungiyar babban birnin ta shafe minti 70 tana gana wa takwarata ta Kataloniya azaba tare da zura mata kwallaye biyu, kafin ta farfado. Godiya ta tabbata ba uban gayya Robert Lewandowski da ya fara farke kwallon farko tare da nuna wa Ferran Torres hanyar kara kwallo na biyu, yayin da yaro dan bauwa Lamine Yamal ya raba gardama ta hanyar cin kwallo na uku. Sai dai Ferran Torres ya sake dawowa inda ya ci kwallon raba ni da yaro bayan da aka yi karin lokaci kafin busan karshe. Ita kuwa Sevilla tana a matsayi na uku bayan da ta yi nasara da kyar 1-0, yayin da Athletic Bilbao  ta karfafa matsayinta na hudu.

Hoto: Kim Hukari/Image of Sport/picture alliance/Newscom

A gasar Premier League kuwa, Arsenal ta yi nasara a wasan da ta yi da Chelsea a gidanta a ranar Lahadi a London, matakin da ya kawo karshen rashin nasara a wasanni uku da ta yi, wanda ya  raunaa matsayinta na biyu. Ita kuwa Manchester United ta yi wa Leicester dukan kawo wuka 3-0, nasarar da ta bai wa kungiyar Ruben Amorim damar zuwa matsayi na goma 13 a gasar Premier bayan wasanni 29. Ita kuwa Chelsea mai matsayi na 4 da maki 49, ta rasa damar yin zarra ga Manchester City, wacce ta yi 2-2 da Brighton. A daya wasan kuwa, Fulham mai matsayi na 8 da maki 45 ta samu nasara 2-0 a gida a kan Tottenham mai matsayi na 13 da maki 34.

Karin Bayani: Labarin Wasanni: Bayern Munich na kan gaba

Hoto: Pierre-Philippe Marcou/AFP/Getty Images

A Serie A kuwa, Inter Milan ta sake samar da tazara a saman teburin gasar kwallon kafar Italiya bayan da ta doke Atalanta da ci 2-0 , yayin da Juventus Turin mako guda bayan ta sha kashi a gida da ci 4-0, ta sake shan kashi da ci 3-0. Ta hanyar cin wannan nasara, Inter ta yi wa Naples ko Napoli nisan maki uku bayan da ta tashi 0-0 a Venice.

Yanzu kuma sai mu zo nan gida Jamus, inda bayan kare jini biri jini da suka yi a wasan mako na 26, Bayer Leverkusen ta tuntsurar da Stuttgart a mintunan karshe da 4-3, tare da haifar da shakku a saman teburin Bundesliga. Kungiyar da Xabi Alonso ke horaswa ta yi amfani da tuntuben da Yaya-babba Bayern Munich ta yi a Berlin inda ta tashi 1-1 da Union, wajen rage rata zuwa maki shida a tsakaninsu. Hasali ma dai, Leverkusen ta koma ga tsohon halinta na kakar wasan karshe, na jiran karin lokaci wajen cire wa kanta kitse a wuta. A yanzu dai, Bayer Leverkusen da ke rike da kambun zakaran Jamus ta yi wasanni 30 ba tare da an doke ta ba a waje ba a gasar Bundesliga.

Hoto: Wolfgang Frank/Eibner-Pressefoto/IMAGO

Ita kuwa Bochum da ke sahun baya ta yi abin kai inda ta lallasa  Eintracht Frankfurt da ci 3-1, lamarin da ya karya gwiwar Frankfurt na yunkurin neman matsayi na uku don samun cancantar shiga gasar cin kofin zakarun Turai na gaba. Ita dai  Eintracht mai maki 45 ta ci gaba da zama a matsayi na hudu, amma tana da maiki iri daya da Mainz, sannan ta zarta RB Leipzig da maki uku, duk da doke Yaya-karama Dortmund da ta yi da ci 2-0. Sai dai Mainz na ci gaba da fafutuka na ganin cewa ta samu gurbi a gasar zakarun Turai ta badi inda a wannan karon ta tashi 2-2 da Freiburg, kuma kamar yadda muka kawo muku a shirin Bundesliga Live a ranar asabar, kwallon karshe da dan wasan Freiburg ya ce na daga cikin wadanda suka fi gamsarwa.

Kungiyoyin mata ‘yan kasa da shekaru 17 na kasashen Afrika sun gudanar da zagaye na biyu na mataki na biyu na share fagen shiga gasar cin kofin duniya ta mata, inda Jamhuriyar Benin da Kenya da Aljeriya suka samu damar hayewa mataki na gaba. 'Yan matan Benin sun mamaye na DR Kwango da 3-0 a Kinshasa, baya ga nasara a wasan farko da suka yi da 2-0, lamarin da ya ba su damar zuwa zagayen karshe na wasannin share fage inda za su kara da Zambiya. Su kuwa 'yan Kenya sun casa takwarorinsu na Yuganda da  3-0, baya ga nasara 2-0 da wasan farko, godiya ta tabbata ga Brenda Achieng da ta ci biyu dagaq cikin kwallayen. Sai dai 'yan wasan Junior Starlets na Kenya na da jan aiki a gabansu a wasa na gaba inda za su yi karon batta da takwarorinsu na Kamaru. A nasu bangaren, 'yan matan Aljeriya sun gasa wa na Botswana aya a hannu da ci 4-0, alhali sun fara shan kashi da ci 2-1 a wasan farko, amma suka cancanci zuwa wasa na gaba. A ranar 27 ga watan Afirilun 2025 ne za a san kasashen da za su wakilci nahiyar Afirka a gasar cin kofin mata 'yan kasa da shekaru 17 da haihuwa da za ta gudana a kasar Maroko.

Hoto: Samuel Shivambu/BackpagePix/empics/picture alliance

Manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Afirka suna shirin ci gaba da fafatwa domin samun tikitin shiga gasar kofin duniya da za ta gudana a Amurka da Kanada da Mexico. Amma dai, 'yan wasan da masu horaswa suka yi gefe da su ko suka ki kira bisa dalilai da dama na haddasa shakku a kasashen da ake ji da su a fagen tamaula a Afirka. A yayin da a kamaru ga misali, rashin kira masu tsaron gida Andre onana, a karawar da za ta yi a Eswatini a rana larabawa mai zuwa yake yamutsa hazo, a Najeriya kuwa, sake cire Dan wasan kwallon Nigeria da a yanzu yake bugawa Kungiyar Kano pillars Ahmed Musa daga cikin rukunin yan wasan ne ke jawo cece kuce. Da farko dai, an saka Ahmed Musa Wanda shine kaftin din Kungiyar ta Super Eagles a rukunin 'yan wasa, amma daga bisani aka cire shi a wasan da Najeriya za ta yi da Ruwanda a ranar Jumma'a.

Hoto: Thomas Klein/DW

Dan wasan tennis Jack Draper na Biritaniya ya doke Holger Rune na Denmark da ci 6-2 da 6-2 a ranar Lahadin da ta gabata, lamarin da ya ba shi damar lashe gasarsa ta farko ta Indian Wells a California din Amurka.  Draper, mai matsayi na 14 a duniya kafin lashe kofi, ya ba da mamaki ta hanyar kawar da mai rike da kofin sau biyu Carlos Alcaraz a wasan dab da na kusa da na karshe, inda ya doke abokin karawarsa a cikin mintuna 69 kacal. A yanzu dai, dan wasan Draper mai amfani da hannu hagu mai shekaru 23 da haihuwa ya haye zuwa matsayi na bakwai a jerin sunayen da ATP ta wallafa a wannan Litinin, amma dan Italiya Janik Sinner na ci gaba da rike matsayi na farko a duniya a fagen wasan tennis.

A rukunin mata kuwa, fitacciyar ‘yar kasar Rasha Mirra Andreeva mai shekaru 17 a duniya ta lashe gasar Indian Wells ta hanyar mamaye lambar dayar duniya 'yar Belarus  Aryna Sabalenka da ci 2-6, 6-4, 6-3. A yanzu dai, duk da cewa Sabalenka na ci gaba da rike kambunta na lamba daya, amma Mirra Andreeca tana a matsayi na shida a jadawalin WTA da aka buga ranar litinin. Dama dai, nasarar da ta samu a Dubai a watan da ya gabata,  ya sanya Andreeva ta zama 'yar tennis mafi karancin shekaru da ta taba lashe gasar WTA 1000.