1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ba mu yarda a wulakanta yan wasanmu ba

Abdullahi Tanko Bala
October 14, 2024

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta mayar da 'yan wasan ta gida bayan zargin wulakanta 'yan wasan a Libya gabanin wasan da za a buga ta neman cancanta a gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika na 2025.

Tawagar 'yan wasan kasa na Najeriya
Tawagar 'yan wasan kasa na NajeriyaHoto: Ubale Musa/DW

'Yan wasan na Najeriya sun yanke shawarar ba za su buga kwallo ba inda suka ce an wulakanta su kamar dabbobi. Jam'ian NFF sun yi dukkan abin da ya kamata na mayar da 'yan wasan gida a cewar Ademola Olajire daraktan sadarwa na hukumar kwallon kafar ta Najeriya NFF.

Hukumar kwallon kafar ta Najeriyar ta aike da korafi a hukumance ga hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF. 'Yan wasan na Najeriya an yi watsi da su ne a wani tsohon filin jirgi inda suka shafe sama da sa'oi 15 bayan da jirginsu ya sauka a wannan Lahadi.

An ruwaito cewa ofishin Jakadancin Najeriya a Libya ba zai iya sanya baki a cikin lamarin ba, har ya sai ya sami izinin yin hakan daga gwamnatin Libya.