1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta kwashe daruruwan 'ya'yanta daga Sudan

Ubale Musa M. Ahiwa
April 27, 2023

A yayin da ake ci gaba da kokari na kwashe daliban Najeriya daga kasar Sudan, gwamnatin kasar ta ce ta kwashe sama da dalibai 2000 ya zuwa kasar Masar a halin yanzu.

Hoto: - /AFP/Getty Images

Manyan motoci 13 ne dai ya zuwa yammacin wannan Alhamis ne suka isa kasar Masar daga Sudan da nufin kauce wa rikicin da ke cikin kasar a halin yanzu. Dalibai kusan biyu da 600 ne dai ake saran za su iso nan a Abuja ya zuwa safiyar ranar Juma'a, a karon farko tun bayan barkewar rikicin. Abujar dai ta ce ta kashe dalar Amurka miliyan daya da dubu 200 da nufin fara aikin kwashe daliban da ragowar ma'aikata na jakandancin kasar ko bayan mata da yara kanana.

Abike Dabiri dai na zaman shugabar hukumar kula da ‘yan kasar da ke kasashen waje, ta ce Najeriyar na kallon tururuwa ta mutanen da ke ta neman hanyar fita kasar a halin yanzu.

“Muna da motoci da suka tafi daga jami'ar kasa da kasa da ke birnin Khartoum da ke da kasa da awa biyu da isa birnin Aswan na kasar Masar. To sai dai kuma wannan tafiya na da sarkakiyar gaske, wani lokaci sai an yanke, kuma a wani lokaci sai an tsaya na lokaci. Wasu motocin suna sun tafi daga jami'ar El Razi ita ma da ke a Khartoum ina jin 13 ne z asu je iyakar Aswan in da jakadan Najeriya a kasar ta Masar da shugaban hukumar agajin gaggawa ke zaman jiran su karbe su.

A gaba daya dai ana saran motoci 40 domin wannan aiki. To sai dai kuma ana fuskantar ‘yar matsala saboda tururuwa ta mutanen da ke son dawowa Najeriya. Kowa na fadin yana son zuwa gida duk da ba mu da rajistarsu. Na fada kuma mutane ba su son su ji, mafi yawa na ‘yan kasarmu da ke a wajen kasar Sudan ne, a cewar Abike Dabiri.

Hoto: ROB ENGELAAR/ANP/IMAGO

Ya zuwa ranar Juma'a ne dai ake saran sahun farko na ‘yan kasar ke shirin isowa zuwa ga Abuja, a yayin kuma da za a ci gaba da kokari na kwashe daukacin yan kasar da ke Sudan. Hankalin mahukuntan Najeriyar a fadar karamin ministan harkokin wajen kasar Ambasada Zubairu Dada za su karkata ne ga yan makaranta da yara kanana ko bayan mata.

To sai dai kuma majiyoyi maras tabbas sun ce wasu a cikin motocin daliban sun makale a sahara inda direbobin motocin ke neman cikon kudi kafin dorawa zuwa gaba a kan hanyar Aswan din.