SiyasaAfirka
Najeriya ta lalata hauren giwaye da dama
January 9, 2024![](https://static.dw.com/image/65483225_800.webp)
Talla
Kimanin shekaru 30 ke nan da mafarauta suka addabi giwayen da ke Najeriya, kuma tuni adadin dabbobin ya ragu matuka daga 1,500 zuwa kasa da 400, sakamakon kashe su da mafarautan ke yi domin su mallaki hauren na giwayen.
Minista a ma'aitakar muhalli ta Najeriya Ishaq Salako, ya shaida cewa gwamnati ta lalata hauren giwayen kuma za ta yi amfani da tokar wajen gina gunkin giwa domin tunawa da mahimmancin giwa wajen muhalli.
Duk da cewa Najeriya ta rattaba hannu a yarjejeniyar kare hakkin dabbobi, kasar ta kasance kan gaba a jerin kasashen da ke kashe dabbobi musamman giwaye da sauran sassan nau'ikan dabbobi zuwa kasashen Asiya.