Najeriya ta lallasa Sudan a rukunin na hudu
January 15, 2022Najeriya ta lallasa kasar Sudan da ci uku da daya, a wasannin rukuni na hudu da ake ciki a gasar kwallon Afirka mai ci a halin yanzu a Kamaru.
Dan wasan Najeriya Samuel Chukwueze ne ya fara zura kwallon farko a ragar Sudan wanda ya zaburar da Super Eagles din, sai kuma Taiwo Awoniyi ya zura ta biyu a ragar ta Sudan kafin zuwa hutun rabin lokaci.
'Yan dakikoki da komawa bayan hutun rabin lokaci, Moses Simon dan Najeriya, ya zura kwallo ta uku a ragar Sudan.
Sudan dai ta ci kwallon nata guda ne a bugun daga kai sai mai tsaron gida da Wlieldin Khedr ya ci mintuna 20 da komawa hutun rabin lokacin.
Yanzu dai Najeriya na da maki shida a wasanni biyu da ta buga ta kuma haye zuwa zagaye na gaba. A ranar Talata ne Najeriyar ta yi wa Masar daya mai ban haushi.