Najeriya ta lashe gasar cin kofin Afirka na mata
December 3, 2016Talla
Najeriya ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka na mata, bayan doke kasar Kamaru da ci daya mai ban haushi. 'Yan wasan Najeriya sun samu nasarar jefa kwallon ana kusan tashi daga wasan.
Wasan wanda ya gudana a birnin Yawunde fadar gwamnati Kamaru, Najeriya ta zira kwallo a raga a mintoti 84, saura mintoci shida kadai a tashi a wasan, abin da ya jefa magoya bayan Kamaru kimanin 40,000 da ke cikin filin wasan cikin bakin-ciki.