1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai karar masu neman kifar da gwamnatin Tinubu

Abdoulaye Mamane Amadou Khadijah Rufa'i(Ubale Musa)
April 21, 2026

Cin amanar kasa ko yunkurin juyin mulki, gwamnatin Najeriya ta gurfanar da wadanda ta zarga da neman kifar da gwamnatin Bola Tinubu a gaban kuliya.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Sarah Meyssonnier/AP/picture alliance.com

Hukumomin Najeriya sun gurfanar da mutane shida a gaban kotu bisa zargin cin amanar kasa da yunkurin kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, wadanda aka gurfanar ciki har da wani tsohon Manjo Janar da jami'in 'yan sanda da tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timpre Sylva, da shi ma ake thumarsa da taimakawa wajen boye wannan shirin na kifar da gwamnatin Tinubu ta kowane hali.

Tinubu ya tsallake rijiya da baya, amma fadar shugaban kasa ta musanta

A watan Oktobar 2025 rundunar sojin kasar ta bayyana cewa an kama jami’an soja 16 bisa wani lamari da ta kira "rashin ladabi da da'a inda a wancan lokaci ta musanta duk wasu bayana na yunkurin juyin mulkin tare da rufa-rufa kan kokarin sojojin na kawar da gwamnatin Tinubu. Amma a watan Janairu, rundunar sojin ta amince da cewa an yi yunkurin juyin mulki a kasar mafi karfin tattalin arzikia nahiyar Afirka, ta kuma sanar da cewa za a gurfanar da wasu jami’ai da ake zargi da kitsa yunkurin.

Tuhume-thumen da ake yi wa wadanda aka kama da kokarin tsorata Bola Tinubu

Babbar kotun kolin Najeriya a Abuja Hoto: Olamikan Gbemiga/AP Photo/picture alliance

Wasu takardun da masu gabatar da kara suka shigar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta nuna yadda ake zargin mutanen da cewa sun yi kulla-kulla a tsakaninsu don cin amanar kasa, sannan kuma ana zargin mutanen da cewa sun san Kanal Mohammed Alhassan Ma’aji da aka bayyana a matsayin jagoran masu kokarin kawar da gwamnatin na tattaunawa da wasu don aikata laifin cin amanar kasa,” amma ba su sanar da hukumomi ba. Sannan wasu karin tuhume-tuhumen sun hada da shirin aikata ta’addanci sai dai kuma har yanzu hukumomin shari’a ko na tsaro ba su fitar da bayani a kai ba.

Najeriya ta taba fuskantar juyin mulki sau biyar a karni na 20, amma ba a sake samun hakan ba tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999. Wannan lamari na zuwa ne yayin da ake samun karuwar juyin mulki a kasashen yankin yammaci da Tsakiyar Afirka, ciki har da kasashen Benin da Guinea-Bissau, inda masana ke danganta hakan da rikice-rikicen zabe, matsalolin tsaro da kuma rashin jin dadin matasa.

Ko yunkurin juyin mulkin najeriya na da nasaba da zaben 2027 da ke tafe a Najeriya?

Alon tallata 'yan takarar zaben shugaban kasa na 2023 a NajeriyaHoto: SAMUEL ALABI/AFP

Fara shari'ar na zuwa ne a yayin da fagen siyasar Najeriya ke daukar dumi a shirye-shiryen babba zaben watan Janairu na 2027, inda shugaba Bola Tinubu ke shirin neman wa’adi na biyu bayan ya kammala wa'adin shekaru shekaru hudu a kan kujerar mulki a kasar da tafi kowace kasa a nahiyar Afirka yawan jama'a da karfin tattalin arziki. Sai dai Najeriya na fama da kalubalen tsaro, inda ’yan ta’adda da barayin daji ke cin karensu babu babbaka shekaru 17 a sassan arewaci da hare-haren 'yan aware a yankunan kudu maso gabascin Najeriya.