1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta rage farashin fetur ga 'yan kasar

March 18, 2020

Gwamnatin Najeriya ta sanar da rage farashin man fetur daga Naira 145 zuwa Naira 125  a kan farashin kowace lita.

Nigeria Lagos Benzinpreis
Hoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

Wannan na nufin ke nan kasar ta rage akalla Naira 20 a kan farashin litar man fetur. Gwamnatin kuma ta ce sabon ragin zai fara aiki ne nan take.

Karamin Ministan Man fetur Timpre Sylva ne ya sanar da wannan mataki a ranar Laraba  kamar yadda  wakilinmu na Abuja Ubale Musa ya ruwaito mana.


Tun a shekara ta 2016 ne dai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kara kudin man fetur daga Naira 87 da ta iske a hannun gwamnatin Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ta kuma mayar da shi zuwa Naira 145 a kan kowace lita, lamarin da ya haddasa cece-kuce a kasar. Ana dai ganin ragin farashin na ranar Laraba ya faru ne  a sakamakon yadda darajar fetur din ta fadi a kasuwar duniya.

Sai dai kuma hukumomi sun ce farashin ka iya sauyawa idan darajar fetur din ta kara dagawa ko kuma ta sauka a kasuwannin duniya.