1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta sake shiga matsin tattalin arziki

Abdul-raheem Hassan
November 21, 2020

Hukumar kididdiga ta Najeriya ta ce tattalin arzikin Najeriyar ya sauka da kashi 3.65 a watanni ukun karshe na shekarar 2020, saboba matsalolin cutar Corona da kuma karyewar farashin man fetur.

Nigeria Geldwechsler
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Tattalin arzikin Najeriya ya sake fadawa tsaka mai wuya karo na biyu cikin shekaru hudu sakamakon annobar Corona da kuma faduwar farashin man fetur a kasuwannin dubniya. A 2016 ne dai Najeriya ta shiga matsin tattalin arziki a karon farko sama da shekaru 20, amma ta farfado a 2017.