An gano cutar shan inna a Najeriya
September 5, 2024Ya zuwa yanzun dai yara kusan 50 ne dai Abuja ta ce sun kamu cikin sabon naü'in cutar Shan Inna da ta sake bulla cikin jihohin arewacin kasar da makwabta. Ministan lafiya Farfesa Mohammed Ali Pate dai ya ce ko bayan Najeriya akwai yaduwar da ta tada hankali har a kasashen Jamhuriyar Nijar da na Chadi.
Karin Bayani: Kawo karshen cutar polio a Afirka
Da kyar da gumin goshi ne dai Najeriyar ta yi nasarar kare cutar shekaru hudu bayan wani dogon gangamin sarakuna da malamai da shugabannin al'ummai. Babbar barazana dai a idanun gwamnatin tarayyar dai na zaman, yiwuwar watsuwa ta cutar zuwa sassan tarayyar Najeriya. Abin kuma da a cewar Farfesa Pate ya tilasta wani yunkuri na kasashen da nufin tunkarar barazanar da ke iya tasiri nan gaba.
Duk da cewar dai babu kiddidiga ta zahiri bisa yawa na shanye gabobi sakamakon cutar ta Polio a tarayyar Najeriyar, cutar ta shan innar dai ta shanye gabobi dubbai cikin kasar a lokaci mai nisa. Kuma sake bullar cutar a tunanin Musbahu Lawal Didi da ke zaman shugaba na kungiyar masu bukata ta musamman, ya nuna cewa batu ne da ya dace a mayar da hankali domin dakile matsalar. Sabon nau'in cutar dai ya bulla ne cikin jihohin Katsina da Kano da Zamfara da Sokoto da jihar Kebbi.