NFF: Najeriya ba za ta kori kocinta ba
November 20, 2020Talla
Rubutun da Ministan Harkokin Wasannin kasar Sunday Dare ya yi ne a Twitter na cewa yana tababa kan kwarewar kocin biyo bayan gazawar Super Eagles ta lashe duk karawar da ta yi a wannan shekarar, ya haifar da jita-jitar cewa a wannan Jumma'ar hukumomin Najeriya za su sallami Gernot Rohr.
To sai dai Shugaban Hukumar Kwallon Kafar kasar, Amaju Pinnick ya sanar a wannan Jumma'a cewa ko kodan ba za su dakatar da kocin ba, yana mai tunasar da masu yada jita-jitar cewa Gernot Rohr shi ne ya jagoranci Najeriya har ta samu damar shiga kofin duniya kuma ta zo na uku a gasar cin kofin Afirka. A bisa wannan Pinnick ya ce Najeriya za ta ba kocin na Super Eagles damar jan ragamar kasar zuwa kofin duniya da kofin CAF da za a yi shekara ta 2022.