1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 60 na 'yanci a Najeriya

October 1, 2020

A cikin halin rashin tsaro da talauci da ma barazanar rabuwa, Tarayyar Najeriya na bikin cika shekaru 60 da samun 'yanci.

Nigeria Feier 60 Jahre Unabhängigkeit
Najeriya na bikin cika shekaru 60 da samun 'yanci daga BirtaniyaHoto: Kola Sulaimon/AFP

Kama daga fareti ya zuwa ga yanka alkaki na biki da sakin tattabaru na lafiya dai, an share tsawon rana ana ta owambe a tsakani na shugabannin Tarayyar Najeriyar da ke bikin cika shekaru 60 da samun 'yanci daga Turawan mulkin mallakar Birtaniya. Ga mafi yawa na 'yan kasar dai, 60 din na zaman shekaru na ritaya bayan hidima ta kasa da kila gudummawa mai tasiri.

Karin Bayani:  Kokarin shawo kan matsalar tsaro a Najeriya

To sai dai kuma ga shugabanni na kasar 60 din ba ta wuci lokacin kallon tsaf da kila samar da makoma a cikin Najeriyar da ta dauki lokaci tana ta rarrafe har ya zuwa yanzu ke neman damar tatata. Kama daga basasar farko ya zuwa mulkin soja da ma annobar cin hanci da ma sabon rashin tsaro na ta'adda, Najeriyar taga fari taga baki da ma rodi-rodi a yanzu sakamakon annoba ta coronavirus.
Abun kuma da ya dauki hankali na shugaban kasar da tun da sanyin safe, ya share tsawon mintuna kusan ashirin yana neman kwantar da hankali na 'yan kasar da ke neman mafitar jerin matsalolin da ke barazana ga rayuwa: "Wadanda suke a gwamnatin baya daga shekarar 1999 zuwa 2015, na da tsauri na idon kokari na soke kokarinmu.  A halin da muke ciki, gwamnatin kirki dole ne ta fuskanci zahiri da  daukar matakai tsaurara. Farashin man fetur zai fuskanci kwaskwarima. Yanzu muna sayar da shi kan Naira 161 kan kowace lita, in mun yi kwatanci  da makwabtanmu zai tabbatar da abun da muke fadi. Kasar Chadi da ke samar da man na sayar da shi kan 362 kan kowace lita, Nijar na sayar da shi kan 346, Ghana tana sayar da shi a kan 326, can gaba kadan Masar tana sai da shi kan 211, ita kuwa Saudiyya na sayar da shi kan Naira 168. babu hankali ace mai yafi sauki a cikin Tarayyar Najeriya fiye da kasar Saudiyya."

Shekaru 60 na lalube cikin duhu?

Karin Bayani: Najeriya: 'Yan kasa cikin kuncin rayuwa

Ko an samu sauyi ci-gaba?Hoto: Paul Almasy/akg-images/picture alliance

To sai dai kuma ko ya gwamnatin kasar ke kallo na adawa, a tunanin 'yan PDP na kasar ba banbamci a tsakanin masu tsintsiya da 'yan lema na kasar, a fadar Sanata Umar Ibrahim Tsauri da ke zaman sakataren jam'iyyar PDP na kasa. Kokari na nunin yatsa cikin gazawa ta kasa dai, ra'ayi na banbamta kama daga dattawan da suka faro tafiyar ya zuwa matasan da ke rawar hantsi yanzu.

Karin Bayani: Najeriya: Barazanar karancin abinci

Salisu Idris dai na zaman wani matashi da ke fadin yana hango haske ga kasar a cikin rutsutsi na rashin hadin kai da ma rashin tsaron. To sai dai kuma a tunanin Alhaji Tanko Yakasai da kasar ta yanke cibiya a idonsa, Najeriyar ta fuskanci tafiyar hawainiya a cikin wa'adin 'yancin. Abun jira a gani dai na zaman taku na gaba ga Tarayyar Najeriyar da ta share lokaci cikin duhu, kuma ke neman mafita a cikin rugugin sauyin da ke kadawa a ko'ina a duniya.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani