1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta tabbatar da shirin Juyin mulki

Uwais Abubakar Idris
January 27, 2026

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa za’a hukunta sojojin da aka samu da hannu a yunkurin juyin mulki a kasar, bayan kammala bincike da ya gano sojoji 16 da hannun a cikin lamarin

Sojin Najeriya cikin shrin ko ta kwana
Sojin Najeriya cikin shrin ko ta kwanaHoto: STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images

Bayan kwashe watani tana musanta yunkurin juyin mulki, a karshe rundunar sojin Najeriya ta tabbatar lallai an yi yunkurin kifar da gwamnatin dimukurdiyya karkashin shugaban Bola Ahmed Tinubu. A sanarwar a Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaron Najeriyar Major Janar Samaila Uba ya fitar, ya ce an kamala bincike kuma wadanda aka samu da laifi za su fuskanci hukunci.

Karin Bayani:Najeriya za ta gurfanar sojojin da ake zargi da shirin juyin mulki 

Wasu sojojin Najeriya a bakin aikiHoto: Mosa'ab Elshamy/AP Photo/picture alliance

Tun a watan Oktoban 2025 ne dai hedikwatar tsaron sojin Najeriya ta sanar da kame sojoji 16 da suka hada da Birgadiya Janar da Kanar, Lantanar Kanar da masu mukamin Kaftin bisa zargin aikata laifuffukan da a lokacin suka ki bayyanawa, duk da  kokarin danganta shi da juyin mulki bai samu amincewar sojojin ba. Shin me yasa aka yi rufa-rufa a wannan lamari da ke da karfi da munin gaske a Najeriyar?

Karin Bayani:Ranar Tunawa da juyin mulki na farko a Najeriya

Gugguwar juyin mulkin soji dai na ci gaba da kadawa a yankin Afrika ta yamma inda kasashe hudu sojoji suka karbe mulki a cikinsu wadanda suka hada da Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Niger, sannan an yi yunkuri a jamhuriyar Benin yanzu kuma ga Najeriya. Me wannan ke nunawa ga dimukurdiyar Najeriyar da ake sam barkar samun dorewarta tun daga1999?

Karin Bayani: Shekaru 60 bayan juyin mulki na farko a Najeriya

Hafsoshin tsaro na kasashen kungiyar Afirka ta yamma ECOWASHoto: Chinedu Asadu/AP Photo/picture alliance

Daukar matakin hukunci a kan sojojin da aka samu da yunkurin juyin mulkin dai hukuncin kisa ne. Wannan na nuna girman laifin tare da fatan ya zama darasi ga masu irin wannan tunani. Tuni Najeriya da wasu kasashe suka fara yunkurin kyautata dimukurdiyya a karkashin kungiyar ECOWAS da ta tarayyar Afrika don shata dimukurdiyyar da ta dace da al’adu da muradun alummun Afrika don kauce wa irin wannan matsala musamman na shugabanni da ke mulkin mutu ka raba wanda Najeriya bata cikinsu. 
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani