1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta yi gargadi kan biyan kudin fansa

January 18, 2024

A yayin da rashin tsaro ke kara ta'azzara a Najeriya, gwamnatin kasar ta ce tana shirin ta hukunta masu tara kudade da nufin biyan fansa ga masu garkuwa da mutane.

Bola Ahmed TinubuHoto: Emmanuel Osodi/AP Photo/picture alliance

Kama daga babban birnin taraiya na Abuja ya zuwa ragowar sakuna da lunguna na Najeriya dai ana kallon ta'azzarar satar al'umma a cikin neman fansa, ko bayan gazawa ta gwamnatin kasar da ke da babban aikin samar da tsaro cikin kasar.

To sai dai kuma masu mulki na kasar sun ce batu na tara kudin fansa ya sabawa doka kuma na iya kaiwa ga hukunci na masu tunani na tausawa kamammun.

Karin bayani: Najeriya: Bukatar girka rundunar 'yan sanda na jihohi

Ministan tsaron kasar Mohammed Badaru Abubakar dai ya ce tara kudaden fansa walau cikin kafar sadarwar ko a tsakani na 'yan uwa ya sabawa doka, kuma baya taimaka wa babban yakin da ke ta sauyin launi cikin kasar a halin yanzu.

Hoto: STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images

Sashe na 14 na dokar satar al'ummar ta 2013 da aka yi wa gyaran fuska a shekara ta 2022 dai ta tanadi dauri na shekaru dai dai har 15 ga masu tu'ammali da kudaden fansar walau bayarwa ko kuma karbarsu cikin neman ceton.

To sai dai kuma wani sashen na 14 amma fa na kundin tsarin mulki na kasar ya baiwa 'yan kasar damar samun kariya ta gwamnati, ko su kare kansu a fadar Barrister Buhari Yusuf da ke zaman wani lauyan da ke zaman kansa a taraiyar Najeriyar.

Hoto: KOLA SULAIMON/AFP

Kokarin komawa doka ko kuma neman mafita ta zahiri, wani sabo na rahoto na kamfanin Beacon Consult mai bin diddigi na satar al'ummar ya ce mutane sama da 4,000 ne aka sace a yayin da aka kashe 9000 da doriya a shekarar da ta shude.

Ko a watan Disamban da ya shude dai mutane 519 ne dai aka sace a cikin Najeriyar abun da ke nuna karuwar da ta kai kaso 11 a cikin 100.

Karin bayani: Matsalar tsaro ta yi kamari a sassan Najeriya

Yahuza Getso dai na zaman kwarre bisa tsaro a tarrayar Najeriyar kuma ya ce sabon matsayi na gwamnatin bashi shirin taimaka wa yakin satar ta 'yan kasa.

Abun jira a gani dai na zaman mafita a tsakanin masu mulki na kasar da ke fadin dole a koma doka, da yan kasar da ke tunanin mafita ta zahiri.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani