1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashe 17 sun tsallaka wasan Turai

Mouhamadou Awal Balarabe SB/LMJ
November 20, 2023

Kasashe 17 na Turai sun samu tikitin shiga gasar Euro ta badi da Jamus za ta dauki bakunci, yayin da dan wasan tennis Djokovic ya kai bantensa a wasan karshe na ATP 2023 a Turin.

Wasan neman cin kofin kasashen Turai da Jamus za ta dauki nauyi
Taken wasan neman cin kofin kasashen Turai da Jamus za ta dauki nauyiHoto: Joaquim Ferreira/picture alliance

Makonni kalilan bayan da takwarorinsu maza suka lashe gasar Super League ta Afirka, 'yan mata Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu sun samu kofinsu na biyu na gasar kungiyoyin da ke rike da kambun zakara a kasashen nahiyar bayan da suka doke 'yan matan SC Casablanca da ci 3-0 a birnin Korhogo. Wannan nasarar dai ba ta zo da mamaki ba, duba da cewar abokan hamayyarsu ba su yi nasarar zura wa 'yan matan Mamelodi kwallo ko da a daya ba tun lokacin da aka fara wasannin rukuni har i zuwa wasan karshe. Hasali ma dai, 'yan Sundowns sun sake karbe kofin da suka rasa ne a gaban AS Far a kakar wasan da ta wuce ba, Sai dai a yanzu sun kafa tarihi saboda su kadai ne suka lashe kofin champions League na matan Afirka karo na biyu. A yanzu dai, 'yan matan Mamelodi sun samu kyautar kudi dalar Amurka 400,000 daga Hukumar Kwallon kafa ta Afirka sakamakon lashe wannan kofi.

'Yan wasan MasarHoto: Weam Mostafa/Sports Inc/empics/picture alliance

​Wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 sun shiga rana ta biyu a shiyyar Afirka a karshen mako. A rukunin farko, Masar ta mamaye Saliyo da 2-0, kuma wannan ita ce nasara ta biyu a wasanni biyu da fir'aunawan Masar suka yi. A rukuni na biyu kuwa, Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta dibi kashinta a hannun Sudan da ci -0-1.  yayin da rukuni na shida Gabon ta cire wa kanta kiste a wuta a karawa da ta yi da Burundi inda ta lashe wasan da ci 2-1. Ita kuwa Aljeria ta doke Mozambik da ci 2-0 a rukuni na bakwai.

Sannan a wasansu na farko na tankade da rairaya, Afirka ta Kudu ta yi nasara a wasan da ta yi da Benin da ci 2-1, yayin da Tanzaniya da lallasa Nijar da ci 1-0.  Senegal kuwa ta murkushe Sudan ta Kudu da ci 4-0. Ita kuwa Kamaru ta doke Mauritius da ci 3-0, yayin da Côte d' Ivoire da za ta dauki bakuncin kofin kwallon kafa na kasashen Afirka ta yi wa Sechelles dukan kawo wuka 9-0.

Ita kuwa  Najeriya bayan da ta tashi 1-1 da Lesotho a ranar farko, ta sake yin kunnen doki da Zimbabuwe 1-1. A halin yanzu dai, makomar Super Eagles na tangal-tangal a fafutukar neman gurbi a gasar cin kofin duniya ta 2026, lamarin da wasu masana kea alakanta rashin kokarin kasar ce da rashin manyan yan wasan da suke taka leda a manyan kungiyoyin turai.

'Yan wasan Sengal da MorokoHoto: Weam Mostafa/empics/picture alliance

A wannan Litinin kuwa,  wasanni tankade da rairaya tara ne za buga ciki har da wasan Gambia da Côte d' Ivoire, yayin da Chadi za ta kara daMadagaska, ita kuwa Mali za ta kece raini da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

A nan Turai kuwa, wasannin share fage na neman shiga gasar kwallon kafa ta nahiyar a bazara mai zuwa a Jamus ne suka gudana. Hasali ma dai, wasanni tara ne suka gudana a rana ta goma kuma ta karshe, inda  wacce tuni ta tabbatar da cancantar shiga gasar ta lallasa Georgia da ci 3-1 a rukunin A. Ita kuwa Beljiyam wacce ita ma ta haye ta mamaye Azerbaijan da ci 5-0. A nata bangaren kuwa, Portugal din Cristiano Ronaldo ta doke Iceland cikin sauki da ci 2-0.

Kosovo da Isra'ilaHoto: Armend Nimani/AFP/Getty Images

Kasashe 17 ne suka cancanci shiga gasar ta Turai a halin yanzu ciki har da Turkiyya, wacce a fafatawar sada zumunta da ta yi a ranar Lahadi ta samu nasara a kan Jamus mai masaukin baki da ci 3-2. Ita kuwa Faransa ta yi ruwan kwallaye da zai iya shiga cikin kundin tarihi inda ta doke Gibraltar da ci 14-0. Sai dai Italiya ta kasance daya daga cikin giwayen kwallon kafa da har yanzu ba ta samu tikitin shiga gasar ba. Amma dai Italiya za ta kara da Ukraine a fafatawar neman matsayi na biyu a rukuninsu, kuma wacce ta yi nasara ce za ta tsallake, saboda Ukraine da Italiya suna da maki 13 kowaccen su.

A sauran wasannin kuwa, Ireland ta Arewa za ta fafata a gida da Denmark, yayin da Slovenia zab ta yi wasanta da Kazakhstan

Novak DjokovicHoto: Antonio Calanni/AP Photo/picture alliance

A fagen wasan Tennis, Novak Djokovic dan kasar Sabiya ya yi abin da sa'arsa bai taba yi ba inda ya lashe kofin ATP a karo na bakwai cikin tarihi a birnin Turin na kasar Italiya. Gwarzon na duniya mai shekaru 36 ya samu nasara a kan Jannik Sinner dan kasar Italiya da ci 6-3, 6-3. Djokovic wanda yanzu shi ne gwani na gwanaye a fagen tennis ya kafa sabon tarihi a muhimar gasa ta ATP, lamarin da ke tabbatar da bajintar da ya nuna a bana a cewar Novak Djokovic:

"Wannan girbi ne ga irin abin da ni da tawaga ta da iyalina muka shuka a wannan shekara, tana daya daga cikin shekarun da na fi samun nasara a cikinta a rayuwata. Na samu nasara hudu a cikin gasannin biyar kuma na yi wasan karshe a Wimbledon. Don haka, ba zan iya neman kari ba, a gaskiya. Ina matukar alfahari da wannan kakar wasa."

Sai dai rashin nasara a wasan na ATP bai karaya wa Jannik Sinner gwiwa ba, maimakon haka ma dai, ya ce ya dauki darisi na ire-iren abubuwa da ya kamata in inganta:

" A yau ban saki jiki sosai a wasu lokuta ba, kuma na ji kamar jikina na da rauni. Kuma kun san a duk lokacin da ka baras da wasa a gaban lamba daya na duniya, akwai bambanci mai girma. Na yi kokarin takaita asarar maki, saboda haka ne na yi ta kokarin kai kora. Amma na yi wasu kurakurai, watakila kuskuren rashin nitsuwa."

Gasar ATP ta Turin na daya daga cikin manyan gasannin tennis da ake rufe shekara da ita, wacce take hada ’yan wasan 8 da suka fi fice a duniya.

Ostareliya ta sake zama zakaran wasan kurket na duniya bayan da ta doke Indiya mai masaukin baki a wasan karshe da ya gudana a Ahmedabad, alhali dukanin hasashe sun bayyana cewar Indiya ka iya lashe wannan kofi. Ita dai Ostareliya wacce ta gaji Ingila, ta bijire wa duk hasashen da aka yi tare da bada mamaki a gaban firaministan Indiya Narendra Modi. A iya cewa ma dai, Ostaerliya ta rama wa kura aniyarta ne saboda ta baras da wasan da ta yida Indiya a wasan rukuni. A yanzu Ostaerliya na da kofuna shida na Kurket bayan nasarar da ta samu a 1987, 1999, 2003, 2007 da 2015 a gasannin duniya 12 cikin shekaru 47.