1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zabi sabbin shugabannin majalisu a Najeriya

Uwais Abubakar Idris GAT
June 11, 2019

A Najeriya an zabi Sanata Ahmad Lawal na jam’iyya mai mulki ta APC a matsayin sabon shugaban majalisar dattawan a yayin da Hon Femi Gbajabiamila ya zamo sabon shugaban majalisar wakilai.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Sanata Lawal ya samu kuri’u 79 a yayin da abokin hamayyarsa a neman wannan mukami Sanata Mohamed Ali Ndume shi ma na jam'iyyar APC da amma ke da goyon bayan wasu 'yan adawa ya samu kuri’u 28 a majalisar mai mambobi 109.

Baya ga zaben shugaban majalisar dattawan, an kuma zabi mataimakain shugaba wanda Sanata Ovie Omo-Agege na jam'iyyar APC mai mulki ya lashe. Sanata Agege ya yi takara ne da Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Sanata Ike Ekweremadu na jam'iyyar PDP da ke adawa. Sabbin shugabannin majalisar dattawan da aka zaba sun zamo shugabannin majalisar dattawa ta tara a tarihin siyasar Najeriyar. 

A bangare daya kuma Majalisar Wakilan Najeriya mai mambobi sama da 300 ta zabi Hon Femi Gbajabiamila a matsayin sabon shugabanta bayan da ya doke abokin hamayyarsa Umar Bago a kuri'ar da 'yan majalisar wakilan suka kada a wannan Talata a birnin Abuja. Zaben shugabannin majalisun Najeriyar na wannan karo na wakanan ne a cikin wani yanayi na takun saka tsakanin 'yan majalisun bangaren masu mulki da na bangaren adawa kan mutanen da ya kamata a zaba a matsayin shugabannin majalisun biyu. 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani