1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta zame abar koyi ga sauran Afirka

Zainab Mohammed AbubakarApril 1, 2015

Najeriya na ci-gaba da daukar hankalin duniya, batu da ya sanya sauran kasashen Afirka fatan ya zame tubali na musayar mulki tsakanin gwamnatoci.

Nigeria - Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/Zuma Press

A nahiyar da shugabanni kan dafe madafan iko ba tare da son mikawa wani na gaba ba, amincewa da shugaba Goodluck Jonathan na Najeriyar na shan kaye tare da mika wa zababben shugaba Muhammadu Buhari mulki, ya samu marhabin a idanun duniya da ma masu sa ido kan zaben kasar.

Najeriyar da ke zama uwa mabada mama a nahiyar Afirkar dai, ta kasance inda duniya ta sanya idanu a zaben na karshen mako da ya baiwa jam'iyyar adawa ta APC nasara. A cewar mataimakiyar sakataren Amurka kan harkokin Afirka Linda Thomas-Greenfield dai, kamata ya yi sauran kasashen da ke nahiyar su bi sawu.

A shekarun baya bayannan dai wasu kasashen Afirka sun taka rawar yabo a fannin tabbatar da demokradiyya, misali a watan Oktoba, zanga zangar adawa ta kawo karshen mulkin sai madi ka ture na shekaru 27 na Blaise Campaore a Burkina Faso, tare da gudanar da zabe cikin lumana a kasashen Malawi da Namibia.

Kazalika kasashen Ghana da Mali da Kenya da Senegal sun gudanar da zabuka tare da musayar mulki ba tare wata matsala ta azo a gani ba.