Najeriya ta zuba kudaden yaki da talauci a Arewa
September 30, 2025
Daga cikin Naira Miliyan dubu 330 da kasar ta ce ta kashe a bana wajen rage radadin talaucin, kaso 78 cikin dari na kudaden sun tafi ne ya zuwa al'ummar ta arewa. Arewacin Tarayyar Najeriyar dai na zaman na kan gaba cikin batun na talauci, hujjar kuma da ake yiwa kallon da ruwa d atsaki da karuwar rashin tsaro tsakanin al'ummar yankin.
Kama daga Sokoto inda kaso 91 cikin dari na al'ummarta ke rayuwa ta Rabbana Ka wadata, ya zuwa Jigawa mai kaso 83, da ma ta Zamfara da ke biya mata dai sashen arewacin Najeriyar yana sahun gaba cikin batun na talauci.
To sai dai kuma Abujar da ta ce ta kashe Naira dubu 330 da nufin tallafa wa talakawan dai ta ce ta yi rawar gani cikin sashen na arewa a shekarar bana. Kuma sashen na arewa ne ya fi samun moriya a kokari na yaki da talaucin in da ya samu kaso 78 cikin 100 na kudaden da kasar ta raba a tsakanin talakawa.
Sabuwar kididdigar da ke zuwa a yayin da arewar ke ta kokarin neman mafitar halin babu dai na daukar hankalin 'yan boko da shugabannin yankin yanzu haka. Kokari na yaki da talauci, ko kuma neman daukin hankali a siyasa dai, rikicin na talauci dai na zaman na kan gaba cikin rashin tsaro da koma bayan yankin yanzu.
Kuma sashen na arewa kuma a fadar Alhaji Salisu Mohammed da ke zaman mataimakin babban daraktan kungiyar kula da ci gaban arewacin kasar ta Northern elders forum na kallon wariya cikin kasar a halin yanzu. Karatun bora cikin rabo na dukiya, ko kuma korafin da ba shi da hujja, ba da tallafin cikin neman kare talauci dai sashen arewacin kasar ba shi bukatar rabon kudi a hannun talakawansa.
A tunanin Ahmed Rabi'u da ke zaman shugaban cibiyar habaka kasuwancin arewacin Tarayyar Najeriyar. Wani taron masu takama da boko a arewar dai na can na kallon hanyoyin fitar miliyoyin al'ummar yankin cikin ruwan na talauci da ke ta kokarin neman hadiye su.