1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan riga-kafin corona

Uwais Abubakar Idris RGB
October 25, 2021

Kungiyar kwadagon Najeriya ta bayyana adawa da matakin tilastawa ma’aikata yin allurar riga-kafin cutar corona kafin samun izinin shiga wajen aiki.

Impfkampagne in Südafrika
Hoto: Siphiwe Sibeko/AP Photo/picture alliance

Batun gindaya sharadi ga ma’aikatan gwamnatin tarayyar Najeriya kan sai sun nuna shedar allurar riga-kafin cutar corona kafin a barsu su shiga wajen aiyukansu da gwamnatin Najeriya ta gindaya, ko kuma su zo da shedar gwajin da ya nuna ba su da cutar, ya sanya tayar da jijiyar wuya a tsakanin ma’aikatan, wadanda ke tsoron rashin yin hakan zai iya sanya a hanasu albashinsu ko daukan wani mataki, abin da ya sanya Kungiyar kwadago ta NLC, shiga cikin lamarin domin a samar da daidaito dama fahimtar juna inji Kamared Ayuba Waba, shugaban Kungiyar kwadagon Najeriyar ta NLC.

Kamared Ayuba WabaHoto: DW/Uwais Abubakar Idris

Gwamnatin Najeriyar na fatan jiffan tsuntsaye biyu da dutse guda daya a kan wannan batu, watau ta samu karin mutanen da suka yi allurar da ake fuskantar jan kafa, sannan ma’aikatan da suke a matakin albashi na 10 zuwa kasa da suka kwashe watani goma suna zaune a gida, su fara zuwa aiki. 

Karin Bayani: Yaduwar sabon nau'in corona a Najeriya

A yayin da gwamnatin Najeriya ke koyi da abin da wasu kasashe na Afrika da kuma Turai suka yi na kara kaimi dama sharudda na lallai ma’aikata su yi allurar riga-kafin, inda tuni wasu jihohi irin na Edo da Kaduna suka bi sahu, Kungiyar NLC na mai jadadda bukatar mayar da hankali a fanin wayar da kan jama’a acewar Kamared Ayuba Waba.

Karin Bayani: Yajin aikin NLC bai samu karbuwa ba

Yanzu ana cike da fatan matakan da ake dauka, za su taimaka wajen kawar da masu jan kafa ga allurar, ganin har wuraren ibada ake bin jama’a a kasar domin tabbatara da an masu riga-kafin cutar ta corona.