Najeriya: Takaddama kan sanya hijabi na wata lauya
December 19, 2017
Firdausi Amara Abdulsalam ta kasance cikin tsaka mai wuya bisa dakatar da ita da aka yi daga kamala karatunta na lauya bisa amfani da hijabi. Hakan dai ya haifar da tayar da jijiyoyin wuya daga bangaren Musulmi a Najeriya inda har ta kai kungiyar Musulmin kasar ta shirya wani taro na fadakar da hukumar makarantar da Firdausin ke karatu.
A taron gangamin da ta gudanar a Legas, guda daga cikin kungiyoyin Musulmin kasar ta yi kira ga hukumar makarantar da ta janye matakinta na korar dalibar mai karantun lauya, matakin da kungiyar ta ce ya ci zarafin Firdausi tare da tauye mata hakki na yin addininta. Bayan kawo hujjoji masu karfi daga cikin littafi mai tsarki na Musulmai da ke nuni da cewa addinin Islama ya tabbatar da cewa sanya hijibi ga mace tamkar addini ne.
Shugabannin Musulunci sun bayyana matsayinsu kan hukuncin da makarantar horar da lauyoyin ta Najeriya ta dauka da cewa ya saba wa dokar tsarin mulkin Najeriyar. A kan haka ne ma shugaban gamgamin Musulmin Parfesa Ishaq Akintola ya yi kira ga illahirin Muslmin Najeriya da su farka daga barci domin daukar matakan da shari'a ta tanada domin fitarwa da Firdausi hakkinta a cikin wannan lamari tun kafin ya fada hannun bata gari.
Shugaban kungiyar Musulmi kabilar Igbo Malam Abdulkabir Muhamadu Ojogbo ya ce kare Musulunci ya zama wajibi ga duk wanda ya amsa sunan Musulmi a doron kasa kuma matukar mace Musulma ce dole ne ta sanya Hijabi domin haka shari'a ta tanada ga Musulmin duniya. Yanzu haka dai lauyoyi da dama ne maza da mata a tarayyar ta Najeriya suka sha alwashin kare a gaban shari'a Firdausin wacce wasu ke kallonta a matsayin wata gwarzuwar mace a kasar.