1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Karin kudin ruwa karin matsi ga talaka

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 21, 2022

A daidai lokacin da tlkawa ke kar fuskntar matsin rayuwa a Najeriya, babban bankin kasar ya sanar da karin kudin ruwa kan bashin da bankuna ke bayarwa ga kamfanoni da daidaikun mutane.

Najeriya | abuja | Kasuwar Tumatir
'Yan kasuwa ba sa ciniki, talakawa kuma ba sa iya sayen kayan masarufi a NajeriyaHoto: DW/S.Olukoya

Ba da jimawa ba ne dai, gwamnatin Najeriya ta sanar da karin kudin harajin nan na VAT, baya ga karin udin hasken wutar lantarki. Ana cikin hakan, gwamnatin ta sanar da karin kudin fiton kananan motoci. An kara kudin albarkatun man fetur da iskar gas, baya ga cire tallafin man. Talakawan kasar na tsaka da kokawa kan yadda al'amura ke kara rincabe musu sakamkon matsi da kuncin rayuwa kasancewar kayan masarufi na kara tsada, sai kwatsam babban bankin kasar ya sanar da karin kudin ruwa na bashin da bankuna ke bayarwa ga kananan kamfanoni da ma daidaikun mutane.

Matakin babban bankin Najeriyar dai, na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ta sanar da mayar da kamfanin man fetur na kasar zuwa mai zaman kansa domin kara samun kudin shiga. A yanzu hka dai, kungiyar masu gidajen burodi a kasar ta tsunduma yajin aiki, sakamkon korafin da 'ya'yanta ke yi na tsadar kayan hadin burodin. Haka abin yake ga masu kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama a kasar, inda suke barazanar shiga yajin aiki bayan na yunkurin hakan da suka yi a baya da ba su kai ga janye jiragen daga sararin subahana na Najeriyar ba gwamnati ta shawo kansu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna