1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan tallafi ga Najeriya

March 17, 2021

Al'ummar yankin Arewa maso Gabashin Najeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu, kan shirin da Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da neman kudi dalar Amirka biliyan daya ga wadanda matsalar Boko Haram ta shafa.

Nigeria Monguna Angriff islamischer Extremisten
Najeriya: Hare-haren ta'addanci a Arewa maso Gabas, sun sa al'umma cikin taskuHoto: picture-alliance/AP/Ocha/Undss

Majalisar Dinkin Duniyar dai ta ce ta kaddamar da wannan shirin neman kudin tallafi ne saboda cike gurbin da ake samu na taimakon abinci da magunguna ga miliyoyin 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu. A cewar Edward Kallon babban jami'in ofishin da ke kula da ayyukan jin kai na majalisar, an samu karuwar 'yan gudn hijira a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya daga miliyan biyu da dubu 800 a shekara ta 2018, zuwa miliyan shida da dubu 500 a shekara ta 2020.

Karin Bayani: An yi jana'izar mutanen da aka kashe a Borno

Majalisar Dinkin Duniyar na fatan samun wadannan makudan kudi daga kasashe da sauran masu bayar da tallafi, domin taimaka wa bayin Allah da ke fama da yunwa da sauran bukatu na rayuwa. To sai dai a tsokaci da al'ummar da aka nufi tallafa wa suka yi dangane da wannan kudi da ake nema, sun nuna damuwa kan cewa duk da irin makudan kudin da ake samu al'umma na ci gaba da shan ukuba.

'Yan gudun hijira na fama da matsaloli masu tarin yawa a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Yawancin wadan aka shirya neman kudin domin tallafa musu, sun nuna damuwa kan yadda irin wannan tallafi ba ya iso wa wajensu yadda ya kamata. Masu lura da yadda ayyukan agajin ke tafiya a yankin, sun bayyana cewa har yanzu ba a samar da sakamako mai kyau dangane da kudin da ake samarwa ba, inda matsaloli na cin hanci da rashin tsari gami da son zuciya ke ci gaba da zama tarnaki na cimma nasarar taimaka wa 'yan gudun hijirar. 

Karin Bayani: 2020 shekara ta musamman ga 'yan Najeriya

Ana dai bayyana fargabar yadda za a iya samar da kudin ganin irin matsatsin tattalin arziki da kasashen da ke bayar da taimakon ke ciki, bayaga kalubalen cutar COVID-19  da ta tilasta kasashe da dama rage kudin da su ke bayar wa na tallafi, abin da ya ke zama wata barazana ga makomar 'yan gudun hijirar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani