1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kama yara ya jefa matsin lamba a Najeriya

Nasir Salisu Zango SB
November 4, 2024

A Najeriya halin galabaita da yaran da aka kama a lokacin zanga-zangar kin jinin yunwa suka shiga na ci gaba da tayar da hazo a ciki da wajen kasar duk da matakin Shugaba Bola Tinubu na yi wa wasu daga cikin su.

Zanga-zanga a Najeriya
Zanga-zanga a NajeriyaHoto: Kola Sulaimon/AFP

Kungiyoyin kare hakkin dan adam da sauran jama'a na ci gaba da kokarin samar da yanci ga matasan nan 'yan zanga zanga da aka kama su suna daga tutar Rasha a lokacin zanga zangar kin jinin yunwa da aka yi a Nigeria, bullar faifen bidiyon yara a harabar kotu cikin wani mummunan yanayi shi ne ya kara rura wutar yin tir da yanayin da aka jefa yaran, yanzu haka dai wasu manyan kusoshin yankin arewacin kasar sun hada kai domin ganin an samarwa da matasan mafita.

Karin Bayani: Tinubu ya soke tuhumar cin amanar kasa ga yaran da aka kama

Zanga-zanga a NajeriyaHoto: Kola Sulaimon/AFP

Yanzu haka dai wasu manyan mutane sun shiga wani taron gaggawa a babban birnin tarayya Abuja da nufin fitar da hanyoyin ceto rayuwar wadannan matasa.Tun bayan bullar faifen bidiyon su suna matagungun a harabar kotu mutane ke ta tofa albarkacin bakin su kan cin zarafi da aka yi wa yaran, an dai kama wadannan yara su kusan 70 galiban daga Kano lokacin zanga-zangar kin jinin yunwa dauke da tutar kasar Rasha matakin da gwamnatin Najeriya take cewar cin amanar kasa ne, duk da cewar an ayyana bayar da wadannan yara beli to amma sharudda da ka'idojin karbar belin ne ya zama sarkakiya wajen cimma muradan samun yancinsu.

Tuni dai iyayen yaran suka fara bayyana gamsuwa bisa yadda salon rikon da aka yi wa shara'iar yaran ya sauya tun bayan bayyanar faifen bidiyon halin da suke ciki. Tuni dai manyan mutane da malamai da sauran al'umma suka fara amsa kiran taimakon yaran har ma kuma an jiyo wata tawagar 'yan boko da lauyoyi daga yankin arewacin kasar na shirye-shiryen karbar maganar kacokan, sai dai kuma wasu sun fara amfani da maganar domin cimma wata manufa ta siyasa.