Mafita kan tsaro a yankin Tafkin Chadi
May 25, 2021Tun bayan kisan Marshal Idris Deby Itno cikin watan Afrilun da ya gabata dai, hankalin shugabanni a daukacin kasashen yankin Tafkin Chadin ke tashe. Chadi a karkashin Marshal Itno dai, na zaman kasa mafi tasiri ga kokarin wanzar da zaman lafiya a daukacin kasashen yankin da ke tsaka a cikin rikici. Duk da cewa sabuwar gwamnatin mulkin sojan Chadi ta yi alkawarin sake girka dimukuradiyya a cikin tsawon wattani 18, har yanzu ana yin dar-dar bisa yiwuwar kai wa ga zaman lafiya cikin kasar da ma a makwabtan da ke kallon Chadin a matsayin bangon gabas makari na ruwa.
Karin Bayani: Mafita ga yankin Sahel da Tafkin Chadi
Shugabannin kasashen Najeriya da Nijer da Kamaru da Chadin da kuma Libiya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai, sun share wunin guda suna nazarin dabarun iya kai wa ga sake saitin Chadin domin biyan bukatar kowa. Kuma kama daga batu na siyasa zuwa ga tsaron Chadi da ma daukaci na yankin Sahel dai, sun mamaye zukata na shugabannin da ke ganin ana bukatar kallo na tsanaki da nufin jan ragama ta Chadi zuwa tudun muntsira.
Shugaba Muhammadu Buhari dai na zaman shugaban kungiyar kasashen yankin Tafkin Chadin, da kuma ya ce ana da bukatar tsaya wa bi sa alkawarin watanni 18 a bangaren sojojin da ke jan ragamar Chadi a yanzu, ko bayan samar da gwamnatin da ke gine a bisa kundin tsarin mulki na kasar: "Bukatar taimakawa gwamnatin Chadi sauke alkawarinta na samar da demokaradiyya a watanni 18 abu ne dake da ba zai sauya ba. To sai dai kuma dole ne a tabbatar da mutunta kundin tsarin mulkin Chadi da shi ne jagoran fassara dangantaka a tsakanin 'yan kasar da gwamnati. Lokacin tafi da shirin sake mika mulkin dole ne ya zamo a karkashin mulkin farar hula. Ta haka ne za a tabbatar da ingancin tsarin sake girka dimukuradiyya da kuma kwakkwaran shirin da zai kai ga gwamnatin da za ta samu karbuwa tsakanin kowa, domin amfanin da Chadi za ta samu."
Karin Bayani: Matsalar tsaro na yawaita a Tafkin Chadi
Tun kusan shekaru 50 da doriya dai, al'ada a kasar ta Chadi na zaman mulkin karfi na tuwo maimakon dimukuradiyya ta 'yan kasar da kasashen yankin ke son su gani. Ambasada Zubair Dada na zaman karamin ministan harkokin wajen Tarayyar Najeriyar, kuma a cewarsa kasarsa na tsoron ci gaban rikicin na Chadi ka iya shafar zaman lafiya a daukacin kasashen yankin Sahel. Ko ta ina kasashen guda shida ke shirin su kai da nufin ceton Chadin dai, babban dodonsu ita ce kasar Libiya da ke zaman daya a cikin 'ya'yan kasashen tafkin da kuma har yanzu ke zaman tunga ta makaman da ake amfani da su wajen tarwatsa zaman lafiya a daukacin kasashen yankin guda shida.
In har Libiyan da babu shugabanci a cikinta na zaman annoba a cikin yankin Sahel, ya kamata a mai da hankali cikin harkokinta a tunanin Musa Alfaki Mahamat da ke zaman shugaban kungiyar Tarayyar Afirka, zaman mafita kan hanyar samar da zaman lafiya cikin kasashen yankin Tafkin Chadin, inda ya ce kawance tsakanin kasashen Tafkin Chadida kuma na G5 Sahel na da muhimmanci da kuma bukatar aiwatar da shi cikin gaggawa. Rikicin rashin tsaron dai na zaman karfen kafa ga kokarin kasashen yankin guda shida na amfani da arzikinsu wajen sauya makomar al'ummar da ke kan gaba cikin tsananin talauci a duniya baki daya.