Zargin hana samun bayanai a Najeriya
August 21, 2018Kungiyar ta Human Rights Watch ta nunar da cewa 'yan jarida da 'yan gwagwarmaya na fuskantar kalubale wajen gudanar da ayyukansu, inda ta yi misali da wani dan jarida da ya shafe shekaru kusan biyu ba tare da an san inda yake ba, da kuma wani mai fafutuka da ya ce an azabtar da shi. Kungiyar ta kara da cewa jefa ‘yan jarida a gidajen kurkuku a kan aikinsu, na zama mummunan sako da gwamnatin Najeriya ke aika wa duniya. Saboda haka ta ce akwai bukatar samar da yanayin da 'yan jarida za su iya aiki ba tare da tsoro ba.
A ranar 16 ga watan Agusta ne kotun Majistare ta Abuja, ta ba da belin Jones Abiri na Jaridar Daily Week da ake bugawa a Yenegoa babban birnin Jihar Bayelsa, shekaru biyu bayan da jami'an tsaro suka kama shi. Sannan a ranar 14 ga watan na Agusta 'yan sanda sun tsare wani dan jaridar na Premium Times, saboda rashin bayyana majiyar labarin da ya wallafa. Dama a watan Janairun shekarar da ta gabata ta 2017 ma, ‘yan sandan sun yi dirar mikiya a ofisoshin Premium Times din a Abuja tare da kame ma'aikatan jaridar biyu.