1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya na taya Tinubu murna

Abdullahi Tanko Bala
March 1, 2023

Sabon zababben shugaban Tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da karbar sakon taya murna, daga shugabannin kasashen duniya.

Sabon zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Hoto: APTN

Mai shekaru 70 a duniya Tinubu zai zamo shugaba na biyar tun bayan sake girka dimukuradiyya a tarrayar Najeirya shekaru 24 da suka gabata. Tinubun dai na da jan aiki na hada kan 'yan  Najeriyar bayan zaben da ya raba jama'ar kan batun addini da ma watakila makomar kasar. Duk da zargin magudi sakamakon zaben na aika babban sako cikin kasar da ke kallon sabuwar guguwar siyasar da ke neman kwace ikon mulki daga 'yan Bokon kasar zuwa talakawa masu zabe.

Farfesa Haruna Yerima na zaman masanin tarihin siyas kasar da ya dauki lokaci yana taka rawa a siyasar kasar, da kuma ya ce zaben ya kare da barin mamaki a wurare daban daban cikin fagen siyasa. A karon farko a lokaci mai nisa dai sakamakon na nuna tasirin masu zabe da suka fito da fushinsu a fili suka sa kuri'a domin korar shugabanni a matakai daban daban. Akalla gwamnoni takwas suka ji ba dadi, yayin kuma da masu zaben suka sallami kusan kashi biyu a cikin kashi uku na daukacin wakilan da ke majalisun kasar guda biyu.

Abin kuma da a fadar Farfesa Husaini Tukur Hassan da ke zaman kwarrare a siyasar kasar ke nuna irin karfin masu zabe a fagen siyasar Najeriyar a halin yanzu. To sai dai kuma in har fagen siyasar kasar na kallon sauyin karfi daga 'yan Bokon kasar ya zuwa yan zabe, rashin yawansu a rumfunan zaben na jawo damuwar da ke da girman gaske ga makomar tsarin da sannu a hankali yake dada nuna alamun girma.

Kaso 26 cikin dari na masu zaben miliyan 87 suka iya kada kuri'a, akasin kaso 43 a shekara ta 2015 da kuma kaso 34 shekaru hudu baya. Abin kuma da ya mayar da shi na kurar baya a lokaci mai nisa. To sai dai kuma a yayin da masu tsintsiya ke tsallen murnar dorawa kan mulkin kasar, tuni dan takara na jam'iyyar Labour Peter Obi ya ce yana shirin ya kama hanyar kotu da nufin ja da sakamakon da ke fadin da ayar tambaya a cikinsa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani