1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauraron shari'a kan zaben shugban kasa

Uwais Abubakar Idris LMJ
May 23, 2023

Kotun sauraren kara kan zaben shugaban kasa a Najeriya, ta ki amincewa da bukatar da jam'iyyun adawa suka gabatar mata na ta bari a yada zaman kotun kai tsaye.

Zaben Najeriya | Peter Obi | Bola Tinubu | Atiku Abubakar
Peter Obi na LP da Atiku Abubakar na PDP na adawa da zaben Bola Tinubu na APCHoto: K. Gänsler/DW, Shengolpixs/IMAGO, EKPEI/AFP

Wannan dai na zuwa ne, bayan da kotun ta tsayar da ranar 30 ga watan nan na Mayu da muke ciki domin fara sauraren gundarin shari'ar da jam'iyyun adawar suka shigar gabanta. Jam'iyyun dai suna kalubalantar zababben shugaban Najeriyar ne, kuma sun hade shari'arsu zuwa wuri guda. Manyan jam'iyyun adawar Najeriya biyu na PDP da Labour dai, na kalubalantar zaben da aka yi wa Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa bisa zargin tafka magudui. Jam'iyyun biyu dai, sun nemi da a yada shari'ar kai tsaye domin tabbatar da adalci.

Ba a wannan karon aka saba fuskantar korafi bayan kammala zabuka a Najeriya ba

To sai dai a lokacin da ya yanke hukunci a kan batun yada zaman kotun kai tsye ga al'ummar kasar, alkalin kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban Najeriyar mai shari'a Haruna Tsammani ya ce a karkashin sashi na 36 na kundin tsarin mulkin Najeriya bai ce tsage gaskiya a shari'a ya danganta a kan watsa ta kai tsaye domin kowa ya ga abin da ke faruwa ba. A cewarsa, da ma can hakan ba ya cikin tsarin shari'ar kasar. A 1999 ne dai lokacin da aka kafa kotun da ta saurari zarge-zargen take hakin dan Adam da aka yi a Najeriyar, ta bari aka yada zamanta kai tsaye a Najeriyar. An dai bai wa bangarorin adawar da ke korafi kan zaben da ma ita kanta jam'iyyar APC mai mulki da ake kara, damar gabatar da shaidu 10 a shari'ar da ke da wa'adin tsawon kwanaki 180 kafin yanke hukunci.