1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Wadanda suka mutu a hatsarin tankar mai sun karu

January 19, 2025

Alkalumma wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin fashewar tankar mai a jihar Neja da ke Najeriya sun karu zuwa mutum 86, a cewar hukumar bayar da gajin gaggawa ta jihar.

Hoto: Sani Maikatanga/AP/picture alliance

Shugaban hukumar bayar da gajin gaggawa ta jihar Neja, Ibrahim Audu Husseini ya ce an yi jana'izar kimanin gawarwaki 86 a tsakanin safiyar Asabar zuwa tsakar dare. Ya kara da cewa, kawo yanzu mutane 52 ke kwance a asibiti sakamakon raunukan kunar da sauka samu a hatsarin.

Lamarin ya auku ne da safiyar ranar Asabar, a yayin da jama'a suka yi tururruwa domin kwasar ganima a lokacin da tankar mai dauke da lita 60,000 na fetur ta tuntsire a kan hanyar Dikko, da ta hada babban birnin kasar Abuja zuwa arewacin jihar Kaduna.

Karin bayani: Mutane kusan 100 sun mutu sakamakon fashewar tankar mai a jihar Neja da ke Najeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya, ya mika sakon ta'aziyyarsa ga 'yan uwa da iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su. Shugaba Tinubu ya kuma bayar da umurni ga hukumomin wayar da kan jama'a da su fadakar da mutane irin hatsarin tunkarar tankar mai idan ta fadi. Ko a watan Octoban bara, fiye da mutane 170 ne suka mutu a irin wannan hatsarin a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya.