1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Najeriya: Yajin aikin likitoci na jawo nakasu

July 26, 2023

‘Yan Najeriya sun fada cikin mawuyacin hali bayan da Kungiyar likitoci masu neman kwarewa suka shiga yajin aiki na sai abin da hali ya yi saboda zargin gwamnati da rashin cika alkawarin na yarjejeniyar da suka cimma ba.

Dr Ibrahim Fori Bwala na duba yaran da ke fama da ciwon tamowa a MaiduguriHoto: ASSOCIATED PRESS/picture alliance

‘Yan Najeriya sun wayi gari da rashin likitoci a asibitocin gwamnati saboda yajin aiki da kungiyar likitocin masu neman kwarewa ta sanar da farawa daga ranar Laraba (26.07.2023). Kungiyar ta bayyana cewa ba ta da sauran zabi illa shiga yajin aiki saboda wasa da hankalinsu da gwamnatin ke kan hakkokinsu da kuma rashin cika alkawarin da ke cikin yarjejeniya da aka rattabawa hannu a kai.

Dr Abdullahi Usman, shugaban Kungiyar likitoci masu neman kwarewa na asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri daga cikin wadanda suka yi taro domin yanke hukuncin shiga wannan yajin aiki. Ya ce: "Akwai wasu korafenmu da muka mika wa gwamnati tun shekara ta 2014, mun ta bin gwamnati a kan wannan korafe amma ba ta yi wani abu ba, wasu ma kwanan nan aka yi su. In ka lura likitoci da malaman jinya na barin kasar nan a dubbansu. Me ya sa ake samun haka? Na daya shi ne rashin biyansu da kyau da rashin kayan aiki da tsadar rayuwa kuma da rashin zaman lafiya.”

Talaka na fargana kan yajin aikin likitoci

Jinya na tafiyar hawainiya a asibitin Maiduguri sakamakon yajin aikin likitociHoto: Stefan Heunis/AFP

Wasu likocin sun amsa kiran Kungiyarsu na shiga yajin aiki, yayin da wasu kuma ke kokarin sallamar marasa lafiya da ke gabansu kafin su ajiye aikin, wanda ba a sa da ranar dawowa ba. Abubakar Goni da ke da zama a Maiduguri ya bayyana fargaba kan wannan yajin aiki da likitoci masu neman kwarewa suka shiga a Najeriya. Ya ce: "Gaskiya ba dadi abin da suka yi nan, ga yanayin da muke ciki, ga tsadar mai, gaskiya ba mu ji dadi ba, ta ina za mu je yanzu?."

Shi kuwa Hussaini Garba Sawaba, wani mai fashin baki kan harkokin yau da kullum, ya ce gwamnatin ne ta jefa mutane cikin wannan hali saoda rashin cika wa likitocin alkawari. Ya ce: " Hukuma ce mai laifi saboda ta san halin da ake ciki da halin da talaka ya tsinci kan sa a ciki na tsadar rayuwa. Su wadannan likitoci da su aka dogara. Shi kuwa talaka da asibitin gwamnati ya dogara ,ba shi da inda zai je, ta ina zai fara?.”

Likitoci da gwamnati na ja-in-ja kan wasu batutuwa

Karancin motocin daukar marasa lafiya na ci wa likitoci tuwo a kwaryaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Wasu 'yan Najeriya na cewa liktocin ba su duba halin da ake ciki na tsadar abinci da rashin kudi kafin su shiga wannan yajin aiki ba ganin yadda al'ummar kasa suka fada halin ni ‘Yasu. Amma a cewar Dr Abdullahi Usman shugaban Kungiyar likitoci ma u neman kwarewa na asitin koyarwa na jami'ar Maiduguri ,su ma fa mutane ne kamar kowa. Ya ce "Kasuwa daya muke zuwa da kowa, gida daya muke zuwa da kowa, mu mutane kafin mu zama likitoci, kuma kai ba ka jin tsoro ka bar rayuwar mutane a hannun likitan da yake da 'yunwa?.”

Ya zuwa yanzu babu wani martani da gwamnatin ta yi a kan shiga yajin aikin da likitoci masu neman kwarewa suka yi inda ‘yan kasa ke mika kokensu ga Kungiyar da ta saussauta, ta janye yajin aiki don sake bai wa gwamnatin dama ko za a dace.