Najeriya: Yajin aikin ma'aikata ya tsayar da al'amura.
September 27, 2018Kungiyar ta ‘yan kodago dai ta tsunduma wannan yajin aikin ne domin tursasa gwamnatin Najeriya ta amince da mafi kankantar albashi na Naira dubu 65.
Tun a bara ne dai hadakar kungiyoyin kwadagon Najeriyar suka fara neman gwamnati ta amince da wannan bukata tasu, ta neman karin mafi kankantar albashi wanda a yanzu ake biyan Naira 18000 sai dai masana da dama musamman a fannin tattalin arziki na ganin cewar ko da gwamnatin tarayya ta amince jihohi da dama al‘amarin zai zame musu katankatana ne ganin yadda har yanzu akwai jihohin da suke kasa biyan albashin ma‘aikata balle ace akai ga cimma yarjejeniyar ribanya shi har sau uku. Kwamarad Kabiru Ado Minjibir shugaban kungiyar kwadago reshen jihar kano ya bayyana dalilinsu na tsunduma wannan yajin aiki.
"Yajin aikin ya samo asali ne sakamakon dakatar da tattaunawa da ake yi akan mafi karancin albashi a kasar har illa ma sha Allahu kamar yadda ministan kodago na kasa ya sanar."
Sai dai masana masu fashin baki kan alamuran yau da kullum irinsu malam Abdullahi Ismail kwalwa tsohon sakataren kungiyar kwadago ta jihar Kano na da ra‘ayin cewar wannan yajin aiki na kungiyar kodagon kiran lamba ce kawai domin a fahimtarsa sun makara.
A bangaren ‘yan kasuwa kuma da yawa na ganin cewar karin albashin ba zai amfana musu komai ba sai ta‘azzarar farashin kaya don haka ne ma malam Abubakar Ibrahim ke cewar da an hakura an shiga adduar samun shugabannin nagari.
Sai dai kuma a ra‘ayin Barrister Badiha Abdullahi lauya mai zaman kanta a kano ‘yan kodagon na da iko da hurumin tafiya yajin aiki ta la‘akari da yadda suke cikin garari.
Zuwa yanzu dai dukkan ma‘aikatun gwamnati da makarantu a rufe suke amma kuma sauran ‘yan kasuwa da masu aikace aikacen da ba na gwamnati ba suna ci gaba da gabatar da ayyukansu.