1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damarar yakar cin hanci a Najeriya

June 13, 2018

A wani abun da ke zaman sauyin taku a batun yaki da cin hanci a Tarrayar Najeriya, wata kotun kasar ta yi nasarar daure tsofaffin gwamnoni guda biyu a tsawon makonni biyu.

Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: DW/I. U. Jaalo

An dai share sama da shekaru 10 ana tafka muhawara da dogon Turanci da nufin kai wa ga tabbatar da gaskiya, tuni ma dai har an fara cire tsamanni ga kokari na samun nasara a wasu. Kafin sabon sauyin da ya kalli tabbatar da laifi kan wasu tsofaffin gwamnoni guda biyu a tsawon makonni biyu kana cikin kotu daya. Kama daga Joly Nyame da ke zaman tsohon gwamnan Taraba ya zuwa Joshua Dariye da ya shimfida mulki a tuddai da kwari na jihar Filato dai, sun kai ga cin amanar al’umarsu a fadar kotun da ta zauna a Abuja ta kuma daure kowane shekaru 14 ba zabi.  

Shaidar kudadan Naira na NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

 

Daukar matakn ba sani ba sabo

Ana dai kallon nasarar a matsayin kafa tarihi a cikin yakin shari’ar da a baya ya fuskanci tafiyar hawainiya a kotunan kasar daban-daban, abun kuma da a cewar Barrister Baba Dala da ke zaman wani lauya mai zaman kansa a Abuja ke da ruwa da tsaki da sauyin tsarin shari’ar da ya kawo sauyin taku a bangaren alkali a kotunan batun cin hanci na kasar. Tafiyar hawainiya cikin yakin cin hanci ko kuma kokari na kare abokai da abokan cin mushe dai, daure gwamnonin da dukkan su ke zaman 'ya'yan jam’iyyar APC  mai mulki dai, daga dukkan alamu na shirin aiken sako  ga daukaci na 'yan kasar. A baya dai masu adawa sun zargi gwamnatin da musgunawa nasu bangaran kadai na 'yan adawa da sunan yakin da cin hanci. To sai dai kuma daure gwamnonin na shirin sauya tunani na daukacin 'yan kasar a bisa aniya ta gwamnatin cikin yaki da cin hancin a fadar Dr Aminu Ahmed da ke sharhi a cikin harkokin zamantakewa na kasar wanda ya bayyana matakin da na babu sani kuma ba sabo a cikinsa. Abun jira a gani dai na zaman nisan tafiyar a kokarin kai wa karshen annobar da ta dauki dogon lokaci tana barazana ga ci-gaban al’ummar ta Najeriya.

 

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani