1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yaki da cutar kyandar Biri a Najeriya

Muhammad Bello
August 16, 2024

Hukumomin lafiya a Najeriya sun tashi tsaye don yaki da cutar kyandar biri wadda yanzu manyan cibiyoyin lafiya suka ayyana da cewar babbar annoba ce ta kuma fara bazuwa a duniya.

DR Kongo | Mpox (2024)
Hoto: Arlette Bashizi/REUTERS

Cutar ta Kyandar Biri yanzu a Najeriya ta fi yin barna a jihar Bayelsa da ke kudancin kasar.

Ko da ya ke dama cutar ta kan bulla kadan kadan a sassan kasashen Afrika, ciki har da Najeriya, inda za ka ga wanda ya kamu da ita na bayyanar da kuraje a jikin sa, sai dai sake bullowar cutar gadan gadan tare da bazuwarta a wasu sassan kasashe, al'amari ne da hukumomin lafiya irin su WHO da ACDC mai yaki da cututtuka a nahiyar Afrika, suka ce cuta ce da bai kamata duniya ta yi sake da ita ba.

Karin Bayani:Cutar kyandar biri ta zama barazana a nahiyar Afirka

Hukumomin lafiya dai a Najeriya, musamman NCDC, ta bayyana yadda cutar ta Monkeypox ke yaduwa a kasar, inda ta ce mutane 39 ne ke dauke da cutar a jihohi 33 da ke fadin kasar, inda ta fidda alkaluman da ke nuna cewar jihar Bayelsa da ke yankin Niger Delta, na kan gaba a yawan masu dauke da cutar a halin yanzu.

Hoto: AP/picture alliance

Jahohin Rivers da Cross River da Enugu da Akwa Ibom, gami da Lagos da Taraba da Adamawa da Kano, da Abuja hukumomi a kasar sun ce ana sa ido kan su.

Dakta Odiano Ahiakame, jami'i ne a hukumar kula da yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya.

Ya ce cutar ta Monkeypox kala biyu ce, akwai wacce ta ke yaduwa a nahiyar Afrika ta yamma,da a ke cewa Clay 2, da Clay 1b wadda ta ke sharafin yaduwa a yanzu, da kuma clay 1 da ke bazuwa a shiyyar Afrika ta tsakiya.

Karin Bayani: An samu wani da ya kamu da cutar Kyandar Biri a Sweden

Dakta Brisbe Seyifa , jamii ne a maaikatar lafiya ta jahar Bayelsa.

Hoto: Dado Ruvic/REUTERS

Ya ce yanzu mun san aikin da hukumar lafiya ta duniya da ma gwamnatin tarayya suke yi, mu a nan ma'aikatar lafiya ta jahar Bayelsa, sashenmu na kula da nazarin cututtuka masu yaduwa a tsaye ya ke.

Karin Bayani: Kyandar biri ta bulla a Kwango

Dakta Kakiri Nwangidibamu, dan jahar ta Bayelsa ne.

Ya ce a nan Bayelsa dai ni dai ban ji ba, ban gani ba, game da wadanda suka kamu da cutar ta Monkeypox, kuma ba ka ji a na Magana kan ta cikin jamaa.

Daga alkaluman da hukumar ta NCDC ta fidda, jihar Bayelsa na da adadin mutane biyar da ke dauke da cutar, Cross River hudu,Ogun hudu, Lagos hudu.Ondo uku sai Ebonyi uku.