1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yan adawa sun shirya tunkarar APC

January 7, 2026

A yayin da ake kara kusantar zabukan 2027, jam'iyyun adawar tarayyar Najeriya na nuna alamun farkawa daga bacci don tunkarar Jam'iyyar APC mai mulki a kasar.

Jam'iyyun adawa a Najeriya sun kudiri aniyar tunkarar APC a zaben 2027
Jam'iyyun adawa a Najeriya sun kudiri aniyar tunkarar APC a zaben 2027Hoto: K. Gänsler/DW, Shengolpixs/IMAGO, EKPEI/AFP

An dai share lokaci ana wata ganawa a tsakanin PDP da tsoho na shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan da jam'iyyar ke fatan tsaya mata takara ta shugaban kasa a zaben da ke tafe, a yayin da daya daga cikin masu takara a Jam'iyyar ADC Atiku Abubakar ke fadin ba shi da niyyar janyewa a takarar. Adawar dai ta fuskanci ukubar APC da ta rika dauke jiga jigan yayanta. 

Kama daga rikicin cikin gida ya zuwa ga bibiyar yan mulki dai, jam'iyyu na adawa a cikin tarayyar Najeriyar sun dauki lokaci suna ji a jiki.

Karin Bayani: Shin jam'iyyu adawa a Najeriya suna iya katabus?

To sai dai kuma a yayin da ake kara kusantar zabuka, akwai alamun PDP da yar uwarta ta ADC da ke cikin gidan adawa na nuna alamun komawa dashi mai rai guda tara.

Uwa PDP da ta gana da tsohon shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan dai, ta ce ta samo tabbaci na goyon baya da kila ma taka rawa ta shugaban da a karkashinsa ne jam'iyyar ta lashi zakin mulkinta na karshe.

Taka rawar ta Jonathan cikin inuwar lemar dai daga dukkan alamu na zaman fatan karshe ga yan gidan na Wadata da suka dauki lokaci suna fuskantar rikici.

Karin Bayani:Kalubalen adawa mai karfi a Najeriya

To sai dai in har PDP na tunanin sake tashi daga suma, can cikin gidan ADC da ke zaman amarya ta adawar, daya a cikin jiga jiganta Atiku Abubakar ne ke fadin bashi da niyar ya janye takara ta shugaban kasar komai runtsi.

Atikun dai na zargin fadar gwamnatin kasar da sabon kitson da ke da burin kai shi zuwa ga ritaya a siyasar kasar.

Tuni dai dama ake hasashen wani sabon kawance tsakanin Peter Obi da ya shigo cikin ADC kwannan da Rabi'u Musa Kwankwaso da ke shirin yabi sahu a nan gaba.

Majiyoyin cikin gidan adawa sun ce ana shirin bude tattaunawa ta mutane takwas da nufin sabon auren da ke da burin kare takarar ta Atiku.

Karin Bayani:ADC: Sabuwar alkiblar adawa a Najeriya

To sai dai kuma Atikun ya ce za‘a gwabza a tsakanin daukacin masu takarar ADC da nufin tabbatar da babban burin jam'iyyar.

Koma wane tasiri masu adawar ke iya yi a kokarin kare iko na masu tsintsiyar tarayyar Najeriyar dai, lokacin da ke akwai na iya kaiwa ga tarnaki bisa babban burin.

Kuma ko bayan nan a tunanin Farfesa Sadeeq Abba dake sharhi cikin batun na siyasa, ana bukatar hada kai a bangaren masu adawar a lokaci kankane.

Najeriyar dai na da tsawon shekara guda da kaiwa ya zuwa sake fuskantar zaben da ke da tasiri a gwagwarmayar neman mulkin kasar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani