Mahara sun kashe mutum 17 a Zamfara
December 24, 2018Talla
Shedun gani da ido sun fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, maharan sun kutsa cikin kauyen Magami akan babura, inda suka rika harbin kan-mai-uwa-da-wabi. Daya daga cikinsu mai suna Kasimu Bello ya ce bayan harin sun kwashi gawarwaki goma sha bakwai da suka yi wa jana'iza.
Kakakin gwamnatin jahar, Mohammed Shehu, ya ce sun soma bincike, kuma za su yi duk mai yiyuwa don gano wadanda suka aikata kisan. Kafin wannan harin na ranar Asabar da ta gabata ma dai, an kai wani hari a ranar Laraba na makon jiya inda mutane ashirin da biyar suka rasa rayukansu.