1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Mahara sun kashe farararen hula 30 a Filato

Abdoulaye Mamane Amadou
April 11, 2022

Rahotanni daga jihar Filato a Najeriya sun nuna cewar fiye da mutane 30 ne 'yan bindiga suka kashe lokacin da suka kai sabbin hare-hare kan mazauna wasu kauyuka hudu na karamar hukumar Kanem. 

Nigeria | 
Hoto: AFP via Getty Images

Mahara sun far wa kauyukan ne kan Babura  inda suka dinga harbe mutane tare da kone gidaje. Wasu mazauna  kauyukan da aka kai  harin sun ce  har zuwa yammacin jiya Lahadi suna kan kokarin gano gawawakin mutane da harin ya  ritsa dasu a kauyukan Kukawa, da Gyambau da kuma Kyaram.

Wakilin mu na jihar Filato Abdullahi Maidawa Kurgwi, ya zanta da Alhaji  Danjuma Sarkin Pawan  Kukawa, wanda kuma ya bayyana masa cewa maharan sun kashe mutane da dama bayan da suka kai farmaki a garin na Kukawa inda suka kashe mutum 24.

Kokarin da wakilinmu na samun karin bayani daga hukumomin tsaro a jihar ta Filato ya ci tura, sai dai wata majiya ta ce an hango motocin jami'an tsaro a yammacin jiya lahadi suna kokarin shiga wuraren da aka kai hare-haren.