'Yan bindiga sun kai hari masallaci
May 10, 2021Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Gambo Isa, ya ce, 'yan bindigan sun riski mutanen kimanin arba'in da bakwai a daidai lokacin da suke sallar Tahajjud, sun yi nasarar yin garkuwa da mutum arba'in daga cikinsu, kafin daga bisani 'yan sanda da 'yan kato-da-gora dama wasu jama'ar gari su bi sahu, sun yi nasarar 'yanto talatin daga cikinsu inji kakakin rundunar amma har yanzu da wasu da ba a gani ba. A daren jiya Lahadi ne, 'yan bindigan suka afka kan masallatan a cikin masallacin da ke garin Jibiya a jihar ta Katsina
Ana zaton 'yan bindigan sun fito ne daga dajin Dumburum na jihar Zamfara da ke makwabtaka da jihar ta Katsina. Jama'a a yankin Arewa maso yammacin kasar, sun koka da yawaitar aiyukan 'yan bindiga da ke sace mutane don neman kudin fansa. Amma masana tsaro na ganin mayakan Boko Haram, da suka kwashi sama da shekaru goma suna yada manufarsu, ne suka yadu zuwa yankin.