1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: 'Yan Boko Haram 129,417 sun mika wuya

December 13, 2024

Hedkwatar tsaro mika wuya da mayakan suka yi ya haifar gagarumin nasara a yaki da ta'addanci.

Babban hafsan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa
Hoto: KOLA SULAIMON/AFP

Hedkwatar tsaron Najeriyar dai ta bakin babbana Hafsan tsaro Janar Chritopher Musa ta ce daga cikin wadanda suka mika wuya akwai mayakan Boko Haram da suka dauki makamai su 30,426 da mata 30,774 da yara 62,265.

Janar Christpher Musa yace kofofin da suka bude na samar da zaman lafiya da kuma yin Afuwa ga mayakan da suka zabi ajiye makamansu tare rungumar zaman lafiya su ne suka bada wannan nasara wacce ta samar da kwanciyar hankali da budewar arziki tsakanin al'umma.

Wani tsohon dan Boko Haram din da ya tuba ya nemi afuwar jama'a yana mai cewa

Wasu matasa yan Boko HaramHoto: DW

"Ina Fatan mutane kauyena su yafe mani kurakuran da na yi musu, Ina fata su yafe mini kurakuraina duka”

To sai dai yayinda wasu ke gaskata samun saukin matsalolin tsaro wasu na ganin zaman su cikin al'umma na da hadari.

Malam Usman Muhammad wani ne da ya sha fama da rikicin Boko Haram da yayi sandiyyar mutuwar ‘yan uwansa yace shirin na da kyau duk da suna jin zafin abin da aka yi musu a baya.

Mayakan Boko Haram da suka tubaHoto: Ute Grabowsky/photothek/IMAGO

Gwamnati ta riga ta yafe musu sannan mutum ya riga ya kashe maka dan uwa ya kashe ma uwa ya kashe ma uba, babu yadda za ka yi da shi sai dai muma jama'a mu yi hakuri mu dau kaddara saboda kaddara mu yi hakuri mu danne zuciyar mu Allah ya bamu zaman lafiya.”

To sai dai Malam Muhammad Matawalle Doka na ganin gazawar hukumomi ne ace an karbi wadannan mayakan a wannan lokaci.

Sansanin yan gudun hijira a MaiduguriHoto: Gilbertson/ZUMAPRESS/picture alliance

"Me ya kawo sulhu idan ba gazawar tsaron ba. Mutane ne wanda suka fito kuma a cikin al'ummar da suke zaune suka kashe al'ummar sannan ake cewa an yi sulhu dasu su dawo cikin mutane suke zauna ”

Shi kuma Sale Bakuro baraden Tikau ta jihar Yobe na ganin hanyoyin da ake yi a baya na shagwaba tubabun mayakan abu ne mai hadari.

"Babu yadda za ayi a kyale wadannan mutane da yakin Boko Haram ya raba su daga matsugununsu kuma a ce za a kula da ‘yan Boko Haram to wane irin zama za a yi, ta yaya za a samu jituwa ta yaya za a samu zaman lafiya tsakaninsu da al'ummar da suke gudun hijra. Ana ma tunanin gwamnati za ta dauki jari ta basu saboda su dawo cikin al'umma”

Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Sai dai Masana da Kungiyoyin na ganin a yi taka tsan-tsan kuma a yi amfani da tsofin mayakan ta yadda za su zama masu amfani da kyautata wa al'umma.

Kwamared Dauda Muhammad wani mai fashin baki ne kan harkokin yau da kullum a Najeriya.

"Fatan mu da burin shine a yi amfani da su ta yadda ya dace wajen tabbatar da cewa wandada suka tuba sun amfana sannan al'umma da suma suka shiga wannan damuwar suka fada cikin matsalar suma sun amfana musamman wajen samar da ababan more rayuwa da ci gaban al'umma.