1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: 'Yan Boko na da hannu cikin matsalar tsaro

December 13, 2023

A karon farko cikin lokaci mai tsawo, gwamnatin Najeriya na zargin wasu 'yan bokon kasar da hannu a cikin matsalar satar mutane da tabarbarewar tsaro a arewacin kasar

Mayakan Boko Haram
Mayakan Boko HaramHoto: picture alliance/AP Photo

 

Duk da cewar masana‘antar ma'adinan tarrayar Najeriyar na da girman da ya kai dalar Amurka miliyan 700,000 har ya zuwa yanzu tana ta baya ga dangi wajen bada gudummawa ga tattalin arziki cikin kasar. Sai dai kuma gwamnatin kasar ta ce yan boko na cikin sana‘ar satar ma‘dinan sannan kuma suna rura wutar rikicin ta'addanci da ma zubar jinin da ta mamaye daukacin masana‘antar yanzu haka.

Karin Bayani: Najeriya: Matsalar tsadar rayuwa da tsaro

Ko dayake ya gaza ambato sunaye balle rawar da kowa ke takawa, ministan ma‘adinan kasar Dele Alake yace yan boko dama jiga jigai na yan kasar ke cikin sana‘ar kwasar ma‘dinan babu ka'ida, sannan kuma ke daukar nauyin tada hankalin da ke faruwa a jihohi masu arzikin ma'adinan. Kalaman ministan na kara fitowa fili da gazawar masu mulkin kasar da ke fadin ga matsalar amma kuma ke karkatar da kai wajen nunin yatsa.

Karin Bayani: Ta'asar rashin tsaro a Najeriya

A karshen tsohuwar gwamnatin 'yar Adu‘a da ta kai ga yin sulhu da masu satar mai a cikin yankin Niger Delta, gwamnatocin baya dai daga dukkan alamu na dada nuna alamun gazawa wajen tunkarar 'yan bokon da ke sana‘ar satar ma'adinan.

Injiniya Ibrahim Isa Aliyu dai na taka rawa cikin sana'ar hakar ma'adinai a tarrayar Najeriya, kuma yace rudun da ke masana'antar yana da girman gaske. A baya dai Abujar ta ksanar da jerin matakai da suka hada da haramta ayyukan hakar ma'adinan ba izini, da ma haramta sauka da tashi jirage cikin jihohi irin su Zamfara. Su kansu kalaman ministan a fadar Kabiru Adamu da ke sharhi kan batun tsaron, sun fi kama da zagi a kasuwa maimakon neman warware takadamar mai girma.